Gwamnatin jihar Kebbi ta kaddamar da aikin gina tashar motoci a Birnin Kebbi wanda kudinsa ya kai Naira biliyan 2.99.
A wajen bikin, sakataren gwamnatin jihar, Alhaji Yakubu Bala Tafida, shi ne ya wakilci Gwamna Nasir Idris, ya ce tashar motar ta lalace har ta zama abin damuwa ga al’ummar jihar.
- Wata Kungiya Ta Wayar Da Kan Mutane Kan Dokar Cin Zarafin Jinsi A Jihar Kebbi
- Zaɓen Cike-gurbi: APC Ta Lashe Zaɓen Kujerar Ɗan Majalisar Tarayya Ta Dandi/Arewa A Kebbi
Ya kara da cewa, Dakta Nasir Idris, ya amince da kaddamar da aikin gina katafariyar tashar mota ta zamani ne domin samar da ingantacciyar hanyar sufuri ga fasinjoji da direbobi da kayayyaki da sauran masu amfani da su da ke zuwa da kuma tashi daga jihar Kebbi.
Kwamishinan Ayyuka da Sufuri, Hon. Abdullahi Umar Faruq Muslim, ya ce aikin ya kunshi gyara da kuma zamanantar da babbar tashar motar domin zirga-zirgar na zamani.
Daga cikin wuraren da za a gina akwai samar da ruwan sha da gina katangar zamani da shagunan zamani da wurin hutawa don masu ababen hawa da sanya allon fitar da bayanai na lantarki da za a iya karantawa da kuma gina gidan abinci.
Kwamishinan ya kara da cewa, idan aka kammala aikin, tashar motar za ta zama cibiyar da ta dace da matafiya na cikin gida da na ketare da kuma hada-hadar dakon kaya da ke fitowa daga sassan kasar nan da makwabciyarmu Jamhuriyar Nijar da Benin.
Hakan zai samar da matsuguni da kwanciyar hankali ga masu ababen hawa yayin da suke jiran hawa zuwa wuraren da za su nufa.
AMIJAPP Nijeriya Limited ne ke gudanar da aikin tare da tabbatar da ingantaccen aiki a cikin wa’adin watanni 12.