‘Yan bindigar da suka kashe wani Sarki a jihar Kwara tare da yin garkuwa da matarsa da wani mutum guda sun rage kudin fansar da suka fada tun da farko daga miliyan N100 zuwa Naira miliyan 40.
Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN), ya ruwaito cewa a ranar Lahadi ‘yan bindigar suka fara tuntubar iyalan Sarkin kan biyan Naira miliyan 100 na kudin fansa.
- ‘Yan Bindiga Sun Kashe Sarki Da Yin Awon Gaba Da Matarsa Da Wasu Mutum 2 A Kwara
- Jami’an Tsaro Sun Kama Ɗan Bindigar Da Ake Zargi Da Kashe Nabeeha
An kashe Sarkin, Oba Olusegun Aremu-Cole, wanda shi ne Olukoro na Koro-Ekiti a karamar hukumar Ekiti (LGA) ta jihar Kwara, a fadarsa a daren ranar Alhamis.
A lokaci guda maharan sun yi awon gaba da matarsa da wani mutum guda.
Da yake magana da manema labarai a yammacin ranar Lahadi, Kehinde Bayode, shugaban kwamitin aiwatar da mulki (TIC) a karamar hukumar Ekiti ta jihar Kwara, ya ce an kama wani da ake zargi.
Ya ce an kama wanda ake zargin ne a garin Eruku da ke karamar hukumar Ekiti ranar Lahadi.
Yayin da yake magana kan kokarin da aka yi na kubutar da matar sarkin da aka yi garkuwa da ita da kuma wani mutum, Bayode ya ce: “Masu garkuwa da mutanen sun tuntubi iyalan.
“Suna neman kudin fansa Naira miliyan 100, wanda a yanzu an mayar da shi Naira miliyan 40.
“Amma har yanzu muna tattaunawa da su kuma a yanzu haka, ina kan hanyar zuwa Koro don samun sabbin bayanai kan tattaunawar.
“Za mu ci gaba da yi muku bayani (‘yan jarida) kan yadda lamarin ke wakana,” Cewarsa a yammacin ranar Lahadi.
Sai dai jami’in hulda da jama’a na ‘yan sanda a jihar Kwara, Toun Ejire-Adeyemi, bai tabbatar da kama ko mutum guda ko wani da ake zargi ba.
“Kwamishanan ‘yan sanda ya tura wata tawagar zuwa Koro-Ekiti domin lalubo wadanda suka aikata laifin.
“’Yan sanda suna aiki tare da sauran jami’an tsaro domin kubutar da wadanda aka yi garkuwa da su.
“Ba a kama shi ba tukuna. Za mu sanar da ku abubuwan da ke wakana yayin da zarar an samu nasarar kama masu laifin,” cewar ‘yansanda.