A yayin da ake shirin shiga shekarar dabbar Loong, bisa kalandar gargajiyar kasar Sin, al’ummar Sinawa mazauna Najeriya, masu kaunar kiyaye da yada al’adunsu ga makwabta da abokansu na Najeriya, sun shirya shagulgula a Abuja, babban birnin kasar.
Wani injiniya dan Najeriya da ya halarci bikin na shekara-shekara a karon farko mai suna Adeshina Adegboye ya bayyana cewa, bikin tamkar wani taron al’adu ne dake kunshe da nau’ikan fasahohin al’ummar Sinawa.
- Li Qiang Ya Tattauna Da Kwararrun ‘Yan Kasashen Waje Dake Kasar Sin
- Shugaban Kasar Sin Da Gwamnatin Kasar Sun Bayyana Ta’aziyya Ga Sabon Shugaban Kasar Namibia
Wannan shi ne karon farko cikin lokuta da dama, da aka zayyana bikin da aka fi sani da bikin bazara, wanda ya fado a ranar 10 ga watan Fabrairun wannan shekara.
Bikin wanda ofishin jakadancin Sin dake Najeriya da cibiyar al’adun Sin dake Abuja suka shirya, ya samu halartar dimbin jama’a, ciki har da daliban makarantun sakandare.
Mahalarta bikin da suka taru a cibiyar al’adun Sin da ke tsakiyar cibiyar kasuwanci a Abuja, sun ji dadin yadda aka nuna al’adun kasar Sin da kuma wasannin fasaha daban-daban na Sinawa da Najeriya.
Jama’ar da suka hada da Sinawa, da ’yan Najeriya, da na sauran kasashe, sun rungumi musayar al’adu, inda suka dauki wani babban hoto dake nuna alamar “hadin kai.”
A waje guda, a yammacin ranar Asabar ne aka gudanar da wani biki a Alkahira na kasar Masar domin murnar sabuwar shekara bisa kalandar gargajiya ta kasar Sin da za ta fada a ranar 10 ga watan Fabrairun bana.
Bikin wanda cibiyar al’adun kasar Sin dake birnin Alkahira ta dauki nauyinsa, ya nuna wasannin kade-kade da raye-rayen na al’adun Sinawa. Matsan Masar su ma sun shiga shagalin a cikin tufafin gargajiya na Sinawa, sun rubuta sunayensu da Sinanci, sun ci abinci Sinawa, kuma sun shiga ayyukan al’adu da suka hada da zane-zane, da yanka takarda da almakashi, da dandana shayi.
Da yake jawabi a wajen taron, darektan cibiyar kuma mai kula da harkokin al’adu na ofishin jakadancin kasar Sin dake Masar Yang Ronghao, ya bayyana cewa, Masarawa na kara sha’awar halartar sha’anin al’adun kasar Sin, wanda ya alakanta shi da bunkasar dangantakar dake tsakanin Sin da Masar a ‘yan shekarun nan.
Cibiyar za ta ci gaba da inganta mu’amalar al’adu da fahimtar juna tsakanin Sin da Masar, a cewar sa. (Mai Fassarawa: Ibrahim Yaya)