Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aike da sakon ta’aziyyar rasuwar tsohon shugaban kasar Namibia Hage Geingob ga sabon shugaban kasar, Nangolo Mbumba.
A madadin gwamnati da al’ummar kasar Sin da ma shi kansa, shugaba Xi ya bayyana alhinin mutuwar Hage Geingob tare da mika ta’aziyya ga ‘yan uwansa da ma al’ummar kasar ta Namibia.
- DA ƊUMI-ƊUMI: Mata Na Gudanar Da Zanga-zanga Kan Tsananin Yunwa Da Tsadar Rayuwa A Neja
- Cibiyar Harbar Kumbuna Ta Xichang Ta Kasar Sin Ta Cimma Nasarar Aiwatar Da Harbi Zuwa Sararin Samaniya Karo Na 200
Bugu da kari, kasar Sin ta bayyana alhinin rasuwar shugaba Hage Geingob na kasar Namibiya, inda ta mika ta’aziyya ga gwamnati da jama’ar kasar, da ma ‘yan uwan marigayin.
Da yake mika ta’aziyya a madadin kasar Sin yayin taron manema labarai na yau Litinin, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Wang Wenbin ya bayyana shugaba Geingob a matsayin tsohon abokin al’ummar kasar Sin wanda aka dama da shi wajen kafawa tare da raya bunkasuwar dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare a dukkan fannoni tsakanin Sin da Namibiya, tare da ba da muhimmiyar gudummawa wajen sada zumunta a tsakanin kasashen biyu.
Ya ce a wannan lokaci na jimami, jama’ar kasar Sin za su tsaya tsayin daka tare da al’ummar Namibiya. (Masu Fassarawa: Fa’iza Mustapha, Bilkisu Xin)