Shugaban hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA, Brig. Janar Mohamed Buba Marwa (rtd), ya ce masu safarar miyagun kwayoyi 15 daga cikin 3,412 da ake tuhuma, an gurfanar da su a gaban kuliya an kuma yanke musu hukunci a shekarar 2023.
Marwa wanda ya yi magana a ranar Laraba a hedkwatar hukumar da ke Abuja, yayin da yake jawabi ga kwamandoji, hafsoshi da jami’an hukumar yayin bikin karramawa da bada lambar yabo, ya ce, wadanda aka yankewa hukuncin sun samu daurin shekaru 168 a gidan yari.
Jimillar Jami’ai 104 da hafsoshi 13 ne da suka nuna bajinta a rabin shekarar 2023 ne aka basu lambar yabo a yayin bikin.