Rundunar ‘yansandan jihar Bauchi ta ayyana neman fitaccen malamin addinin musulunci a jihar, Imam Idris Abdul’aziz Dutsen Tanshi ruwa a jallo bisa zarginsa da kin mutunta kotu.
Kuma an sanya tukuici mai gwabi ga duk wanda ya tona inda malamin yake boye a halin yanzu.
- Guterres Ya Gabatar Da Sakon Murnar Sabuwar Shekara Ta Kasar Sin
- Kotu Ta Umarci Gwamnatin Tarayya Ta Kayyade Farashin Kayayyaki Cikin Kwanaki 7
‘Yansanda a wata shelar musamman da ta fitar a ranar Alhamis ta ce, umarnin ya fito ne daga ofishin sufeto-janar na hukumar, inda suka roki dukkanin wani ko wasu da ke da bayanin yadda za a kama Idris da ya gaggauta sanar da jami’in ‘yansanda mafi kusa da shi.
Sanarwar ta ce Idris da ake nema ruwa a jallo sama ko kasa na da shekaru 62 a duniya, kuma an masa gani na karshe ne a adireshin Dutsen Tanshi da ke Bauchi amma yanzu ba a san inda yake ba.
“Da zarar ka ganshi, kama shi ka mikashi ga caji ofis din ‘yansanda mafi kusa da kai ko kai tsaye zuwa ofishin mataimakin kwamishinan ‘yansanda, shafin binciken manyan laifuka na rundunar ‘yansandan jihar Bauchi ko a kira lambobin waya; 08151849417, 09048226246.”
Rundunar ta ce akwai tukuici ga duk wanda ya taimaka musu suka cafke malamin.
Idan za a tuna dai babban kotun shari’a mai lamba 1 da ke Bauchi ta bai wa ‘yansanda umarnin cafko malamin gami da gurfanar da shi a gabanta bisa zargin da kin mutunta gayyatar da kotun ta masa domin cigaba da sauraron karar da ake masa kan tada zaune tsaye da ke barazana ga zaman lafiya a jihar Bauchi.
Malamin dai ya yi abun da ya kira ‘Hijira’ ne bayan da hadakar jami’an tsaro suka yi wa gidansa kawanya da nufin kama shi.