‘Yan’uwa Musulmi assalamu alaikum warahmtullahi ta’ala wa barkatuh. Barkan mu da Juma’a, da fatan Allah ya karbe mu da falalarsa. A wannan makon za mu tabo abin da ya shafi tarihin manyan bayin Allah domin al’umma ta yanzu ta yi koyi daga alheran da suka shimfida a Musulunci da zamantakewa.
A wannan makon ne ake gudanar da gagarumin taron murna da cika shekara 124 da haihuwar Shehu Ibrahim Inyass, a babban birnin tarayya Abuja. A kan haka, za mu yi waiwaye adon tafiya game da gudunmawar da shehin ya bayar ga ci gaban musulunci a karne na 20.
- Zanga-zangar Kano da Neja: Fadar Shugaban Kasa Ta Fara Shirin Dakile Hauhawar Farashin Kayan Abinci
- Babu Inda Na Ce Na Fi ‘Yan Nijeriya Shan Wahalar Tsadar Rayuwa -Ɗangote
Shehu Ibrahim Inyass (RTA), Gwarzon Musulunci ne da ba a yi kamar sa a duniyar Musulunci ba a karne na 20. Shi ne Sahibul Faidhati wanda aka haifa a Kaulakha; ranar Alhamis 15 ga watan Rajab, Hijira tana da shekara 1318, daidai da shekarar miladiyya ta 1898 (Kamar yadda Shehun ya rubuta da hannunsa).
Domin bitar irin alherorin da muka samu na ci gaban Musulunci da wayewar kai daga wannan shehin malami, za mu yi tsokaci dan kadan game da ayyukansa da kuma nasarorin da Musulunci ya yi a duniya a lokacin rayuwarsa.
Sai dai, kafin mu shiga cikin tarihin rayuwar shehin, za mu fara da bayyana yadda Annabi (SAW) ya bayar da dama a yi tarihin Salihan Bayin Allah.
Kamar yadda ya zo a cikin hadisi, Annabi (SAW) ya ce duk wanda ya rubuta tarihin wani Mumini, kamar ya raya Muminin ne. Saboda za a yi ta karantawa ana jin wannan Mumininin. Duk wanda ya karanta tarihin kuma; kamar ya ziyarci Muminin ne.
Saboda wannan magana ta Annabi (SAW) sai malamai suka yi ta rubuta tarihin manya na cikin Musulmi. An fara tun daga kan tarihin Shugaban Muminai, Annabi (SAW) zuwa Sahabbai (RA), da Tabi’ai har zuwa kan manyan malamai duk gabaki daya.
A bisa hakan, an rubuta tarihin Shehu Ibrahim Inyass (RA) da yawa don a rika karantawa kamar yadda wannan hadisin ya koyar da mu.
Wani malami ya fadi cewa “izini ya zo a cikin wani hadisi daga Annabi (SAW) cewa a yi tarihin haihuwar Muminai. Don haka ku dinga yin tarihin Muminai. Idan kana son hujja ta Alkur’ani (in ji malamin), ya ishe ka ayar da Allah ya ce wa Annabi (SAW) “muna ba ka labaran Annabawa…” sannan ga na sauran salihai duk baki daya”. A kan hakan malamin ya ce yin tarihin Bayin Allah Salihai ba bidi’a ba ce a cikin shari’a, kuma duk wanda ya ce bidi’a ce ku karyata shi tare da jahiltar da shi (ma’ana shi jahili ne).
Saboda haka mun gode wa Allah da muka taru a wannan wata na Rajab a wannan wuri mai albarka domin yin Mauludin Shehu Ibrahim Inyass (RA).
Abin da ya sa ake yin Mauludin Shehu Ibrahim shi ne: Shehu Ibrahim Shehun Musulunci ne gaba daya musamman mu a nan Afirka, haka malaman duniya suka nada shi (RA). Idan ya yi fatawa a Musulunci duk Musulmi sun bi saboda Shehun Musulunci ne baki daya.
Ya yi littafai a cikin Shari’ar Musulunci kamar mashahurin littafin nan nasa ‘Raf’ul Malami’. Haka nan Shehu Ibrahim Shehun Imani ne (Makamul Iman). Ya yi magana a kan Tauhidi tare da rubuta littafai a kai kamar littafinsa mai suna ‘Sarimul Ahmadi’ da sauran su. Har ila yau, Shehu Ibrahim Shehun Ihsani ne (Makamul Ihsan). Ya yi magana a kan Sufanci da rubuta littafai a kai kamar littafin da ya rabuta ‘Kashiful Ilbas’ da sauran su.
Haka nan ya yi littfai a sauran fannonin ilmi kamar Sira, Sarfu, Tafsir, Fatawowi, Diwanansa a cikin Yabon Annabi (SAW) da Yabon Shehu Tijjani Abul Abbas da sauran malamai, da wakokin karatuttuka bila’adadin, bayan wasiku (na warware wa malamai mishkilolinsu na addini) da addu’o’i da sauran hikimomi. Duk wadannan ba a boye suke ba ga duk Musulmi.
Musulmi sun kashi kashi ukun nan da muka ambata. Akwai wadanda a matakin Musulmi kawai suka tsaya kamar wadanda suka yi ilmin Fikhu amma ba su kai mataki na gaba ba. Akwai wadanda kuma sun dara zuwa mataki na Imani, bayan sun yi ilimin fikhu sun kuma yi ilmud Tauhidi (Ilimin Tahuhidi). Sai kuma wadanda suka dara nan, su ne wadanda bayan sun yi ilmin Fikhu da na Tauhidi sannan sun san ilmin Sufanci (shi ne ilmin Ihsani). To Shehu Ibrahim (RA) shehun duk wadannan mukaman ne na Musulunci. Ba a taba samun malamin da ya yi littafai a Fikhun Musulunci da Tauhidin Imani da Sufancin Ihsani kamar sa ba.
Don haka in dai akwai adalci, wanda ya tsaya a matakin farko kawai na Musulunci bai gane abin da Shehu Ibrahim ya fada a matakin Imani ba ko wanda bai gane me Shehu ya fada a Sufanci ba, don ya bata Shehu malamai ba za su daga ido su kalle shi ba. Saboda bai san Tauhidi ba ballantana Sufanci. A iya inda ya sanin ma Shehu Ibrahim shehinsa ne.
Yana daga cikin gagarumin jihadin da Shehu Ibrahim (RA) ya yi ba tare da makami ba musuluntar da dubban maguzawa a Ghana. Shehu ya je Tamale a jirgi amma saboda yawan jama’a jirgin ya kasa sauka sai aka wuce Yendi aka sauka a can. Shehu da kansa ya fadi cewa “na lakana wa dubban mutanen da ba za su kirgu ba Kalmar Tauhidi (La’ilaha’illallah Muhammadur Rasulullah). Imamu Hassan (Jikan Shehun) ya ce ya taba gani a cikin gidan tarihi na Ingila an rubuta cewa mutum 4,000 (dubu hudu) ne suka shiga Musulunci a wannan ranar a lokaci guda a hannun Shehu (RA). Su kuma Ghana sun ce mutum 12,000 (dubu goma sha biyu) ne suka musulunta.
Bayan haka, idan muka dauki misali a matakin farko na Musulunci. Shehu Ibrahim (RA) ya komar da Musulmi musamman na Afirka zuwa ga Littafin Allah Alkur’ani da Sunnar Annabi (SAW), ma’ana ‘Kitabu Was Sunnah’ da bin hanyar Salihai Magabata tun daga kan Sahabbai har Tabi’ai da wadanda suka biyo baya (RA). Shehu Ibrahim ya sha wuya a kan wannan. Abin nufi a nan shi ne, Shehu Ibrahim ya koyar da mu mu dinga bin asalin shari’a kar mu sandare a bisa reshe. Kar mu sandare kawai a kan abin da fakihai kadai suka fada ba tare da duba asalin wurin da suka debo ba.
Da irin haka ne ya mayar da duk Afirka ta rika yin kabalu a sallah wanda a da mutanen yankin kaf sake hannu suke yi a sallah. Kar wanda ya ji tsoron fada cewa Shehu Ibrahim ne ya koyar da Afirka yin kabalu a sallah saboda Sunnar Manzon Allah (SAW). Ya sha wuya wajen fakihai har wasu ma sun rika fada masa miyagun maganganu ciki har da masu kafirta shi. Wasu kuma suka ce Bashafi’e ne ba Bamalike ba ne. Haka nan shi ne ya koyar da mutanen Afrika su rika fadin ‘kad kamatis sallatu’ sau biyu a cikin ikamah da kuma daga hannu wajen yin kabbarbarin sallah a wuraren nan guda hudu.
Haka nan, ya koyar da tsayar da gemu (tsaka-tsaki) irin yadda Annabi (SAW) yake yi. Shehu Ibrahim (RA) ya tilasta wa almajiransa tsayar da gemu har aka san su da shi (gemun) wanda a cikin Malikancin Afirka ba a tsayar da gemu. Hakazalika, ya koyar da almajiransa su rika karanta Hadisai musamman Bukhari saboda idan ya kawo musu hukunci kan wani abu su san a ina ya dauko musu. Amma a da ba haka ake ba, sai dai a rika karanta furu’a (littan fikhu), idan za a fadi zancen Hadisi; sai dai ka ce leka cikin mudawwalatu za ka gani. Mudawwalatu a nan suna nufin Hadisai. Ta bangaren Ayar Alkur’ani kuwa, da an dan fadi gutseranta sai a ce karanci ayar da tsawonta ka ji.
Alherin da Shehin ya koyar a duniyar Musulunci ba su tsaya nan ba. Shehu Ibrahim ya hori almajiransa da su dinga yin saukar Alkur’ani a cikin Sallar Tarawihi lokacin Azumin Ramadhan. A wajen almajiran Shehu aka fara ganin haka a Kaulaha. Sannan ya karfafa yin haddar Alkur’ani maigirma. Albarkar Shehu da kafa makarantun da ya yi, an samu sauki sosai wajen yin haddar Alkur’ani. Bayan haka, Shehu (RA) ya koya mana ‘yancin zabi a cikin addini ta yadda kowa zai bi hanyar da yake ganin zai tsira.
A mako mai zuwa za mu cigaba daga inda muka tsaya cikin yardar Allah (SWT). Wa sallallahu alal fatihil khatimil hadi wa ala alihi hakka kadrihi wa mikdarihil aziym.