Miliyoyin ‘yan Nijeriya na ci gaba da fuskantar matsalar karancin hasken wutar lantarki sakamakon wasu dadaddun matsaloli da suka dabaibaye bangaren wutar lantarkin Nijeriya.
Yayin da hukumomi ke ci gaba da daura laifin matsalar ga masu barnata bututu da ke janyo karancin samun gas, hakan na sanya jama’a cikin matsatsi da rashin jin dadin rayuwa.
- Za Mu Tabbatar Kotu Ta Hukunta Dakataccen Kwamishinan Zaben Adamawa Hudu Ari – Fintiri
- An Gama Aikin Bitar Liyafar Bikin Bazara Karo Na 5 Ta Kasar Sin
Wata mai shago a Jihar Legas, Adeola Adewumi, ta ce kusan kowace mako sai sun samu wannan matsalar. Ta ce kayan abincinsu da dama na lalacewa saboda babu firjin da za su adana kayan abincin a ciki.
Karin matsalar wutar lantarkin da ake fuskanta na zuwa ne a daidai lokacin da al’ummar kasa ke kukan matsatsin rayuwa sakamakon hauhawar kayan masarufi da tsadar man fetur. Duk da cewa masu ruwa da tsaki da gwamnati mai ci sun yi alkawarin kawo sauyi a bangaren, amma matsalar na kara kamari.
Ministan wutar lantarki, Adebayo Adelabu, ya shaida hakan yayin ganawarsa da masu ruwa da tsaki a bangaren. Ya ce, tabbas gwamnati na sane da alkawuran da ta yi na shawo kan matsalolin da suka dabaibaye bangaren wutar lantarkin Nijeriya. Ya ce suna iya bakin kokarinsu wajen ganin an samu sauki da shawo kan wannan matsalar, musamman na kawo karshen karancin samun gas.
Sai dai kuma masu ruwa da tsaki sun ce matsalolin harkokon wutan lantarki sun jima a kasar nan ba wai a wannan karon bane da suka samu asali daga lalacewar muhallai, karyewar layukan wuta, bututun gas da sauran matsalolin.