A daren ranar Laraba ne ’yan wasa Sinawa 37 daga lardin Zhejiang suka nishadantar da masu kallo Sinawa da ’yan Tanzaniya da kayataccen wasan kade-kade da raye-raye na shagalin murnar bikin bazara a Dar es Salam, babban birnin Tanzaniya.
’Yan wasan Tanzaniya sun hade da mambobin kungiyar wasan kwaikwayo ta Zhejiang don gabatar da wasannin murnar bikin bazara, ko sabuwar shekara ta kasar Sin, a dakin taro na cibiyar taron kasa da kasa ta Julius Nyerere da kasar Sin ta gina.
- Al’ummar Kano Na Mutuwa Da Yunwa Da Fatara – Gwamna Yusuf
- Shugaban Miyetti Allah, Abdullahi Bodejo Mutum Ne Mai Yi Wa Nijeriya Fatan Alhairi
Wasannin da ’yan wasa Sinawa suka gabatar sun hada da kade-kade, raye-rayen gargajiya da siddabaru da dai sauransu, domin murnar kyakkyawar abota tsakanin Sin da Tanzaniya.
Yayin da su kuma ’yan wasan Tanzaniya suka gabatar da raye-raye na zamani da wake-wake da tsalle-tsalle dake nuna yanayin zamantakewar Tanzaniya daban-daban.
Mataimakin ministan al’adu, fasaha da wasanni na kasar Tanzaniya Hamis Mwinjuma ya bayyana cewa, “dangantakar dake tsakanin Tanzaniya da Sin ta kasance mai zurfi da aminci, shi ya sa ba kawai mu’amalar harkokin siyasa da tattalin arziki muke shiga ba, har ma da sha’anin zamantakewar al’umma irin wannan.” Yana mai jaddada aniyar Tanzaniya na ci gaba da yin hadin gwiwa tare da gwamnatin kasar Sin wajen inganta dangantakar dake tsakanin kasashen biyu. (Mai Fassarawa: Muhammed Yahaya)