ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Saturday, July 25, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Shugaban Miyetti Allah, Abdullahi Bodejo Mutum Ne Mai Yi Wa Nijeriya Fatan Alhairi

by Bello Hamza
2 years ago
Miyetti Allah

Kungiyar Fulani Matasa ta Nijeriya (FUYAN) ta yi tir da ci gaba da tsare Alhaji (Dr) Abdullahi Bello Bodejo yanzu kusan fiye da kwanaki 14 kenan ba tare da sanin halin da yake ciki ba.

Alhaji Bodejo, mutum ne da ya tsayu wajen fatan alhairi ga kungiyar Miyetti Allah Kautal Hore da kuma Nijeriya gaba daya.

  • Fintiri Ya Dakatar Da Jigilar Kayan Aikin Gini Daga Adamawa Zuwa Kasashe Makwabta
  • Abuja Na Fuskantar Baranazar Tsaro -Majalisar Dattawa

kungiyar Miyetti Allah Kautal Hore ta kasaa da Bodejo ke shugabanta, kungiya ce da ta tsayu wajen tabbatar da kare al’adu da muradun al’umma Fulani a fadin tarayyar Nijerya. kungiya ce da aka yi wa rajista da hukumar yi wa kungiyoyi da kamfanoni rajista a Nijeriya (CAC) tana kuma bin dukkan dokoki da ka’idojin da hukuma ta sanya na tafiyar da kungiyoyi irinta a Nijeriya.

ADVERTISEMENT

 

An samu nasarar kafa kungiyar ne bayan kiraye-kiraye daga wasu kungiyoyin Fulani da suka nuna bukatar a samar da babbar kungiya da za ta jagoranci sauran kananan kungiyoyi a fafutukar kare al’adun al’ummar Fulani a Nijeriya. Dalilan kafa kungiyar Miyetti Allah Kautal Hore sun kuma hada da:

LABARAI MASU NASABA

Gwarzo Na Shirin Sake Fitowa Domin Kawo Sabbin Salon Siyasa A Kano

Madallah Da Hutu Ga ‘Yan Sakandire Domin Azumi 

  • Samar kungiyar da za ta hada kan dukkan sauran kungiyoyin Fulani tare da kare al’adun al’ummar Fulani a Nijeriya.
  • Samar da mambobi masu girmama tare da mutunta shugabanni da sarakunan gargajiya na Fulani.
  • Hada kai tare da tafiya tare da wasu kungiyoyi don ciyar da Nijeriya gaba.
  • Tabbatar da hadin kai da tafiya tare da sauran wasu kungiyoyi.
  • Taimaka wa manbobin kungiyar wajen dogaro da kai.
  • Taimakawa wajen yada al’adun Fulani musamman yaren Fulani.
  • Bayar da gudunmmawa wajen ayyukan ci gaba a garuruwan Fulani.
  • Bayar da gudummawa wajen jin dadin al’ummar Fulani tare da mutunta juna.
  • Tabbatar da kiwon dabbobi cikin lumana da zaman lafiya da kuma zaman lafiya tare da dukkan sauran al’ummonin Nijeriya.

Bababn kudurin kungiyar Miyetti Allah Kautal Hore a karkashin shugabancin Alhaji (Dr) Abdullahi Bello Bodejo shi ne hada kan al’umma Fulani don su zama tsintsiya madaurin ki daya.

Ba zaka taba samun mamban kungiyar Miyetti Allah Kautal Hore yana shiga harkokin rarrabuwan kai ba, domin cikakken ma’anar ‘Kautal Hore’ shi ne hadin kai tare da tafiya tare da dukkan al’ummar Fulani a dukkan sassan kasar nan.

Ta hanyar kungiyar Miyetti Allah Kautal Hore Shugaba Alhaji (Dr) Abdullahi Bello Bodejo ya taimakawa al’ummar NIjeriya da dama ta hanyar biya musu kudin makaranta, kudin asibiti, gina makarantu, gina masallatai da kuma samar wa matasa aikin gwamnati a sassa daban-daban, ya kuma yi haka ne ba tare da nuna banbanci ba, a gare shi, shi shugaba ne ga kowa da kowa.

Ya kuma kafa kungiyar ‘yan sintiri mai suna ‘Nomad bigilante Group’ don kawo karshen yadda ake bata wa Fulkani suna. Ga kuma wasu dalilain da ya sa aka kafa kungiyar ‘yan sintirin.

Sun hada da samar da zaman lafiya a yankuna karkara, don taimaka wajen tattara bayanan sirri don kawo karshen sace-sacen shanu a yankuna karkara da kuma kare rayukan manoma da makiyaya. Sauran dalilan sun kuma hada da bukatar samar da tsaro ga gonaki da rugan kiwon shanu da wurin kiwo, haka kuma kungiyar tana samar da kiwon lafiyan da kuma kai agajin gaggawa a wuraren da aka samu wani iftila’i.

kungiyar ta samu nasara a bangarori da dama sun kuma ba mara da kunya wajen gudanar da ayyukan jin kai da kare dukiya da rayukan al’umma.

Ganin irin ayyukan alhairi da Alhaji (Dr) Abdullahi Bello Bodejo yake yi wa al’umma da kuma irin gudummawar da ya bayar wajen kafa wannan gwmanatin muke ganin wannan kamun da aka yi masa tamkar wulakanci ne ga al’ummar Fulani ba na Nijeriya kadai ba har ma na duk duniya baki daya.

Yanzu fiye da makoi biyuj ke nan, muna kira ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya gaggauta sako mana shugabanmu, musamman ganin har yanzu iyalai da masoyansa basu san halin da yake ciki ba har zuwa yanzu.

Amb. Suleiman shi ne sakataren watsa labarai na kungiyar Miyetti Allah Kautal Hore

Miyetti Allah
Bello Hamza
+ postsBio
  • Bello Hamza
    https://hausa.leadership.ng/author/bello-hamza/
    Yunkurin Dauda Lawal Na Bunkasa Bangaren Ma’adanan Jihar Zamfara
  • Bello Hamza
    https://hausa.leadership.ng/author/bello-hamza/
    Shugaban Miyetti Allah, Bodejo Ya Karyata Zargin Halatta Kudin Haram A Zaman Kotu
  • Bello Hamza
    https://hausa.leadership.ng/author/bello-hamza/
    Kafa Cibiyar NIPHID: NCDC Ta Yi Kuskuren Fahimtar Ƙudirin Dokar
  • Bello Hamza
    https://hausa.leadership.ng/author/bello-hamza/
    Uwargidan Shugaban Ƙasa Ta Ƙaddamar Da Muhimman Ayyukan Ci Gaba A Jihar Jigawa

MASU ALAKA

Gwarzo Na Shirin Sake Fitowa Domin Kawo Sabbin Salon Siyasa A Kano
Siyasa

Gwarzo Na Shirin Sake Fitowa Domin Kawo Sabbin Salon Siyasa A Kano

April 25, 2026
Madallah Da Hutu Ga ‘Yan Sakandire Domin Azumi 
Ra'ayoyi

Madallah Da Hutu Ga ‘Yan Sakandire Domin Azumi 

March 18, 2025
Ya Kamata A Biya Yaran Da Aka Gurfanar Saboda Zanga-Zanga Cikakkiyar Diyya – Ajiyan Yawuri
Ra'ayoyi

Ya Kamata A Biya Yaran Da Aka Gurfanar Saboda Zanga-Zanga Cikakkiyar Diyya – Ajiyan Yawuri

November 10, 2024
Next Post
Shagalin Bikin Bazara: Yana Jagorantar Al’ummar Duniya Murnar Sabuwar Shekarar Dabbar Loong

Shagalin Bikin Bazara: Yana Jagorantar Al’ummar Duniya Murnar Sabuwar Shekarar Dabbar Loong

LABARAI MASU NASABA

Tsakanin Digiri Da Sana’a Wanne Ya Fi Muhimmanci A Wannan Lokacin?

Tsakanin Digiri Da Sana’a Wanne Ya Fi Muhimmanci A Wannan Lokacin?

July 25, 2026
Miyetti Allah

Sojoji Sun Kamata Ƴan Bindiga 5 Da Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane A Yobe

July 25, 2026
Gwamnatin Jihar Kano Za Ta Fara Aiwatar Da Shirin Inshorar Lafiya Ga Jaruman Kannywood

Gwamnatin Jihar Kano Za Ta Fara Aiwatar Da Shirin Inshorar Lafiya Ga Jaruman Kannywood

July 25, 2026
Miyetti Allah

Ku Buɗe Wuta Kan Duk Wanda Kuka Gani Ɗauke Da Bindiga – IGP

July 25, 2026
Idan Aka Cire Bangaren Man Fetur Kannywood Ce Ta Fi Samar Da Aikin Yi Ga Matasa —Hamisu Iyantama

Idan Aka Cire Bangaren Man Fetur Kannywood Ce Ta Fi Samar Da Aikin Yi Ga Matasa —Hamisu Iyantama

July 25, 2026
Kogin Kumadugu Ya Yi Ambaliya Karon Farko Cikin Shekara 100 A Yobe

Jihohi 28 Da Abuja Na Fuskantar Hadarin Ambaliyar Ruwa —Rahoto

July 25, 2026
Miyetti Allah

Ƴan Bindiga Sun Sace Shugaban Ƙaramar Hukumar Bungudu

July 25, 2026
Yadda Jami’an Tsaro Suka Fatattaki ’Yan Ta’adda A Wasu Jihohin Nijeriya, Sun Kama ‘Yan Kasar Pakistan Bakwai

Yadda Jami’an Tsaro Suka Fatattaki ’Yan Ta’adda A Wasu Jihohin Nijeriya, Sun Kama ‘Yan Kasar Pakistan Bakwai

July 25, 2026
Miyetti Allah

Obasanjo Da Atiku Sun Sake Musayar Zafafan Kalaman Zargin Juna

July 25, 2026
Manufofin Tattalin Arzikin Gwamnatin Tinubu Sun Lalata Rayukan Al’ummar Nijeriya —ADC

Manufofin Tattalin Arzikin Gwamnatin Tinubu Sun Lalata Rayukan Al’ummar Nijeriya —ADC

July 25, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.