Gwamnatin Tarayya ta yaba wa ‘yan wasa da mai horar da su da jami’an ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Super Eagles saboda rawar da su ka taka na kaiwa matakin ƙarshe a gasar cin Kofin Ƙasashen Afrika na 2023 (AFCON).
Ministan Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya rattaba wa hannu a ranar Litinin, inda ya ce: “Kun ɗaga tutar Nijeriya, kuma kun yi gumurzu har zuwa wasan ƙarshe.
- ‘Yan Kasuwar Singa A Kano Sun Musanta Zarge-zargen Ɓoye Kayan Abinci
- AFCON 2023: Ekong Ya Lashe Kyautar Gwarzon Dan Wasa Duk Da Rashin Nasarar Nijeriya A Wasan Karshe
“Duk da yake mun so a ce mu ne muka yi nasara, a ce mun ɗauki kambun kofin AFCON a karon farko cikin shekaru goma, amma hakan ba ta samu ba.
“Mun yi amanna da ku tun daga farko har zuwa wannan matakin, kuma za mu ci gaba da yin amanna da ku. Mun san cewar a nan gaba ma za ku fi burge mu. Za mu ƙara yin hoɓɓasa.”
Ministan ya ƙara da cewa, “Shugaba Bola Ahmed Tinubu da dukkanin ‘yan Nijeriya Maza da Mata mun ji daɗin ƙoƙarin da ku ka yi.
“Kaiwa wasan ƙarshe da mu ka yi a karon farko tun 2013 shaida ce cewa babu abin da zai gagari Nijeriya idan muka haɗa kanmu a matsayin ƙasa ɗaya mai alƙibla ɗaya a bisa hukuncin Allah.
“Ina addu’ar Allah ya albarkaci Super Eagles. Allah ya albarkaci Jamhuriyar Tarayyar Nijeriya.”