Gwamna Babagana Zulum na Borno ya ce sabuwar kasuwar Banki da aka yi wa kwaskwarima kuma aka mayar da ita ta zamani za ta habaka kasuwancin kan iyaka da kuma ba da gudummawa ga tattalin arzikin Nijeriya da kasar Kamaru.
Zulum ya bayyana haka ne a lokacin da yake bude kasuwar wacce ta’addancin mayakan Boko Haram ya lalata kuma ya tilasta kulle Kasuwar.
- Wuraren Shakatawa Na Beijing Sun Gabatar Da Shagulgulan Al’adu 109 Albarkacin Hutun Bikin Bazara
- Gwamnonin PDP Sun Buƙaci Gwamnatin Tarayya Ta Magance Matsalar Taɓarɓarewar Tattalin Arziki
Kasuwar wacce ke da iyaka da kasar Kamaru, ta kunshi shaguna 128 da kuma wuraren kasuwanci kusan 440.
Zulum ya ce, kasuwar an tanadar da kayan aiki na zamani kamar ruwa da tsaftar muhalli inda ya ce za ta rika daukar ‘yan kasuwa, za ta karfafa harkokin tattalin arziki da samar da ayyukan yi ga mazauna yankin wadanda mafi yawansu rikicin Boko Haram ya ɗaiɗaita.