Shugaba Bola Tinubu ya ganawa da gwamnonin jihohi a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
Taron ya samu halartar mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima da mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu.
- Nan Da Makonni Uku Ɗalibai Za Su Fara Karɓar Bashi Daga Gwamnatin Nijeriya
- Ronaldo Ya Buga Wasa Na 1,000 A Tarihi A Karawarsa Da Al-Fayha Jiya Laraba
Taron wanda bai rasa nasaba da yanayin tsadar kayayyakin abinci da tabarbarewar tsaro a kasar, ya samu halartar gwamnoni sama da 27 da mataimakin gwamnan Bauchi.
Gwamnatin tarayya ta fara fitar da ton na hatsi iri-iri zuwa kasuwanni a wani bangare na kokarin samar da abinci, mai rahusa da sauki a fadin kasar nan.
Hakazalika, an dauki matakan cafke masu boye ahinci da nufin matsa wa al’umma ta hanyar hadin gwiwa tsakanin sojoji da sauran hukumomin tsaro.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp