Halin matsi da tsadar abinci da ake fama da shi a fadin Nijeriya, musamman a yankunan Arewa; ya sa wasu daga jihohi suka fara yin kukan kura ta hanyar yin bore; domin nuna rashin amincewarsu.
Duk wanda ya kwana ya tashi a wannan kasa, ya san irin halin da aka tsinci kai a ciki; musamman a bangaren tsadar da abinci da sauran kayan masarufi.
- Shugaba Tinubu Ya Gana Da Gwamnoni Kan Ƙalubalen Da Nijeriya Ke Fuskanta
- Nijeriya Za Ta Shawo Kan Ƙalubalen Da Take Fuskanta Nan Gaba Kaɗan – Ganduje
Mutane daga bangarori daban-daban na na tofa albarkacin bakinsu, dangane da wannan matsala da ta kunno kai; a cikin masu wannan jajantawa, har da su kansu gwamnoni da sarakuna da sauran masu fada a ji.
Har ila yau, wasu na dora alhakin wannan al’amari da tashin gwauran zabi da dalar Amurka ta yi, ganin cewa kusan komai namu a Nijeriya na da alaka da ita, wasu kuma na ganin cewa, baya ga tashin dalar har da batun cire tallafin man fetir da gwamnatin tarayya ta yi a shekarar da ta gabata da kuma matsalar su kansu ‘yan kasuwa.
Haka zalika, a wannan mako da muke ciki ne, Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu, ya shelanta cewa; gwamnatinsa ta sanya dokar ta-baci a bangaren harkokin noma, domin Nijeriya ta samu damar iya ciyar da kanta tare da fitar da wani bangare na abincin zuwa kasashen waje, don sayarwa.
Shugaban Kasar, ya yi wannan furuci ne a yayin da yake karbar bakuncin tawagar wakilcin Shugabannin Kungiyar Tijjaniya, bisa jagorancin Khalifa Muhammad Mahe Niass, a fadar shugaban kasar da ke Abuja. Ya kuma yi alkawarin kafa hukumar kayyade farashi.
Wannan furuci tare da albishir na shugaban kasa, ya zo ne a daidai wannan lokaci da wadannan abubuwa suka rincabe, kowa yake tofa nasa albarkacin bakin.
Ga rahotannin da wakilan namu suka tattaro mana dangane da matakan da wasu gwamnonin suka fara dauka, domin magance wadannan matsaloli na rayuwa.
Kano
Halin Matsin tattalin arziki da hauhawar farashin kayan abinci da na masarufi da aka tsinci kai a ciki ya sa a Jihar Kano, Shugaban Hukumar Sauraron Korafe-korafe da Almundahanar Kudade, Barista Muhyi Magaji Rimin Gado bayar da sanarwar cewa, yanzu haka wannan hukuma za ta fara aikin binciken ajiyar kayan abinci, musamman wadanda aka jibge domin kokarin kara musu farashi.
Bayan mako guda da bayar da wannan sanarwa ne, tawagar shugaban hukumar ta yi wa kasuwar abinci ta Dawanau dirar mikiya, inda ya isa bakin wani rumbun tara abincin ya bayar da umarnin cewa, cikin minti 10 kacal mai wannan wuri ya zo ya bude ko kuma a karya mukullin wajen, babu shakka wannan mataki ya fara kwantar da hankalin masu karamin karfi tare da taka wa matsalar hauhawar farashin da ke addabar mutane birki a wannan jiha.
Shi ma a nasa bangaren, Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusif; ya bayyana matukar damuwarsa kan mummunan tashin hankalin da al’umma ke ciki, inda ya ce; “ko shakka babu al’umma na fama da matsalar yunwa”. Saboda haka, a kokarin lalubo hanyoyin saukaka wa mutane wannan hali da suke ciki, gwamnan ya gana da kungiyar ‘yan kasuwa daga bisani kuma ya karbi bakuncin Shugaban Rukunin Kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, wanda ya ziyarci gwamnan; domin taya shi murnar samun nasarar da ya yi.
Kaduna
A bangaren Gwamnatin Jihar Kaduna kuwa, babban mai bai wa gwamnan jihar shawara ta musamman a kan harkokin yada labarai a kafafen Rediyo da Talabijin, Malam Dahiru Ahmed ya bayyana wa wakilinmu cewa, har yanzu dai gwamnan jihar ba ta riga ta fitar da wata sanarwa a kan matakin samar da wata hanya ta magance wannan matsala ga talakawan jihar ba.
Haka nan ya kara da cewa, gwamnan bai riga ya fitar da wani tsari a kan wannan lamari ba, amma akwai yiwuwar a mako mai zuwa ya fitar da wani tsari, wanda zai taimaka wa talakawan don samun sauki kan wannan matsi na ruyuwa.
Katsina
Har ila yau, shi ma Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umar Radda ya bayyana cewa, matsalar kuncin rayuwa da tsadar abinci a kasuwanni, wanda a kullum yake kara ta’azzara; ya zama wajibi a dauki matakin gaggawa a kai ko kuma al’amarin ya cinye jama’a baki-daya.
Gwamnan, ya yi wadannan kalamai ne a lokacin da ya kira wani taron gaggawa da ‘yan kasuwa da jami’an tsaro da sauran masu ruwa da tsaki, game da wannan matsala ake fuskanta a daidai wannan lokaci.
Radda ya ce, “Dalilin kiran wannan taro shi ne, domin na ji daga bakin wadanda abin ya shafa kai tsaye, wato ku ‘yan kasuwa da kuma jami’an tsaro tare da yin amfani da duk abin da kuka bayar na shawara, wanda zai taimaka mana wajen magance wannan matsala da ta taso”.
Gwamnan ya ce, a bisa bayanan da yake samu, an nuna masa cewa akwai hanyoyi da dama da suke jawo wannan matsala, wadanda suka hada da fitar da abinci zuwa Kasar Nijar da Mali da kuma Libya ta amfani da manyan motoci, sakamakon faduwar da kudin Nijeriya ya yi, nasu kuma suna kara yin daraja, wannan ne yasa suke zuwa da kudi kadan suna daukar abinci da yawa su tafi da shi, ana kai wa kasashe da dama.
Yobe
Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni ya jagoranci wani taron gaggawa a kan tsadar abinci da matsalar boye kayan abincin tare kuma da takaita masu safararsa a jihar zuwa wasu jihohi a ranar Asabar da ta gabata.
A taron ya nuna matukar damuwarsa a kan yadda ‘yan kasuwa ke boye kayan abinci tare da na masarufi, lamarin da ke haifar da karancin su tare da jawo wahalhalu ga al’umma.
Matsayar da taron ya cimma a karkashin nasa ya bayyana cewa, gwamnatin jihar ta dauki matakin duba yanayin yawan ‘yan kasuwa masu zuwa sayen kayan abinci a kasuwannin jihar.
Haka zalika, Gwamnatin Jihar Yobe; za ta hada kai da bangarorin jami’an tsaro, domin duba ayyukan ‘yan kasuwa marasa kishin kasa, wadanda ke yin safarar kayan abinci daga kasuwanni.
Haka zalika, sanarwar ta kara bayyana cewa, nan ba da jimawa ba gwamnatin za ta fitar da kwararan matakai, domin dakile illar tsadar kayan abinci tare da sauran kayan masarufi.
Kazalika, gwamnatin jihar ta ba da umarnin gudanar da irin wadannan matakai da taruka a kananan hukumomi 17 da ke fadin jihar baki-daya, don tabbatar da aiwatar da manufofin da gwamnatin jihar ta dauka.
Borno
Haka nan, Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum; shi ma ya dauki matakin kokarin dakile matsalolin karancin abinci tare da tsadarsa, inda ya raba tallafin kudi Naira miliyan N225 da kayan abinci ga iyalai 70,000 a garin Bama da ke jihar.
Zulum ya shiga garin Baman ne a ranar Asabar da ta gabata, inda ya yi kwanaki biyu yana gudanar da raba kayan jinkai da kuma hada kan jami’an tsaro, domin tattauna yadda za a inganta tsaron al’ummar jihar baki-daya.
Haka zalika, a ranar Lahadin da ta gabata; sama da mata 45,000 ne suka ci gajiyar tallafin kudi Naira 5000 ga kowace daya daga cikinsu, yayin da kowane magidanci kuma ya rabauta da samun Naira 25,000 da kuma buhun shinkafa daya da na masara shi ma guda daya.
Gwamnan ya jaddada cewa, gwamnatinsa za ta fi bayar da fifiko kan raba kayan abinci da tsabar kudi a matsayin tallafi ga mutanen da ayyukan ‘yan ta’adda ya shafa da kuma mazauna yankin da ke fafutukar biyan bukatun rayuwarsu.
Neja
Sakamakon wannan matsi na rayuwa da tashin farashin kayan abinci, Jihar Neja na daya daga cikin jihar da matasa suka jagoranci yin zanga-zangar lumana, wanda wannan na daya daga cikin dalilan da ya sa gwamnatin jihar ta umarci jami’an tsaro da su cafke duk wata motar safarar abinci da ta ratso jihar.
Hon. Garba Ibrahim, shugaban kungiyar masu safarar kayan abinci ta kasa reshen jihar, a wata takardar manema labarai da ya fitar a makon jiya, ya umarci mambobinsu da su dakatar da safarar kayan abinci sakamakon kama wasu motocinsu da jami’an tsaro su ka yi, wanda ya bayyana cewa; ko da gwamnatin jiha ta sanya wannan doka, to fa ba ta tuntube su ba, illa kawai dai sun ji sanarwar ta kafafen yada labarai.
Wani mai yin sharhi a kan al’amuran yau da kullum, Alhaji Awaisu ya bayyana cewa; wannan yunkuri da wasu gwamnoni suka fara yi, tamkar yunkurin karya guiwar manoma ne.
Haka zalika, batun runbun hatsi na gwamnati; burga ce babu komai a ciki, domin tallafin da gwamnatin tarayya ta bayar na abinci, kudade ne ta bai wa mazabu su sayi abinci, kenan idan akwai abincin a ajiye; a can ya kamata a debo a raba wa mutane.
Don haka, shawarata ga gwamnatin tarayya da na jihohi ita ce, ya kamata su samar da kamfanonin samar da takin zamani da sauran kayan aikin gona, ta yadda manoman za su iya yin noma cikin sauki, a wannan lokacin ne gwamnati za ta iya daidaita farashi, amma hanyar da ake bi yanzu; ba mai bullewa ba ce.
Har ila yau, wasu sassan ba su da wannan abinci; sakamakon matsalar tsaro dole sai an kawo masu, sannan su kuma jami’an tsaro; an bude musu wata hanya ta yin yadda suka ga dama ga manoma.
Bugu da kari, har izuwa yanzu da aka sanya wannan doka, babu wani abu da ya canja daga karin fashin wannan abinci a kasuwanni kamar yadda bincike ya tabbatar.
Bauchi
A Jihar Bauchi, tun bayan shiga yanayin matsin tattalin arziki da al’umma ke yin a kansa, gwamnatin jihar tare da hadin guiwar gwamnatin tarayya sun raba tallafin shinkafa da kuma rage wa ‘yan fansho kudadensu.
Har ila yau, Gwamnan Jihar Bala Muhammad, a ‘yan kwanakin nan ya kaddamar da fara aikin wasu muhimman hanyoyi da nufin rage wahalhalun fito da amfanin gona da kuma saukaka harkokin sufuri, domin rage wa jama’a matsatsin rayuwar da suke fama da shi.
Bugu da kari, a cewar jami’an gwamnatin jihar, akwai tallafin taki; wanda gwamnatin ta samar ga manoma domin rage kara rage wannan radadi.
Haka zalika, Gwamna Bala ya yi kira ga daukacin al’umar jiharsa da su sanya kishin jiha a gaba tare da hada kai da gwamnati da jami’an tsaro, don yaki da ‘yan ta’adda da kuma bata-garin da ke barazana ga zaman lafiya da walwalar al’umma.
Gwambe
Ita ma Jihar Gombe, ta mayar da hankali wajen lalubo hanyoyin nema wa al’ummanta saukin wannan yanayi da ake ciki na rayuwa, inda Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya, ya fito da wasu tsare-tsare na taimaka wa talakawa da ya hada da samar da tallafin noma, tallafa wa ma’aikata da dubu goma-goma a matsayin karin albashinsu a duk wata da nufin rage kaifin wannan matsi na tattalin arziki.
Da ya ke yin karin haske ga wakilinmu kan kokarin da suke yi, daraktan yada labarai na fadar gwamnatin jihar, Malam Ismaila Uba Misilli, cewa ya yi; tun lokacin da aka samu kai cikin wannan yanayi gwamnati ke buga-bugar nema wa al’ummarta sauki.
“Jihar Gombe, na cikin jihohin gaba-gaba wajen raba tallafi wa talakawa. Tallafin da ya hada da na kayan abinci da sauransu. Kazalika, kafin nan ta raba tallafin taki cikin farashi mai rahusa ga al’ummarta, domin su samu damar yin noma da kuma samun sauran kayan noman.
Ya kara da cewa, “Mutanen da suke yi wa gwamnati ayyuka ko kwangila, ana kokarin biyan su domin kudin ya sake komawa hannun al’ummar jihar.