ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Tuesday, November 18, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Karya Fure Take Ba Ta ’Ya’ya

by CMG Hausa
3 years ago
Karya

Sau da yawa an sha jin zarge-zarge dake nuna yatsa, ga yadda kasar Amurka ke tsoma baki, da sanya hannu dumu-dumu cikin harkokin gidan sauran kasashen duniya da nufin cimma buri na siyasa.

Shaidun gani da ido sun tabbar da sa hannun Amurka wajen kifar da halastattun gwamnatoci a kasashen duniya da dama, wanda hakan ke jefa al’ummun irin wadannan kasashe cikin mummunan hali na jin kai.

  • Maimakon Maimaita Bukatar “Samarwa Kai Kariya” Kamata Ya Yi Amurka Ta Nazarci Ainihin Dalilin Kafa Huldar Diflomasiyya Tsakanin Ta Da Sin

A baya bayan nan, an jiwo tsohon mashawarcin gwamnatin Amurka a fannin tsaro John Bolton, na shaidawa ’yan jaridu cewa, ya taimakawa kasarsa wajen shirya dabarun kifar da gwamnatocin wasu kasashe.

ADVERTISEMENT

Wannan ba abu ne mai ban mamaki ba, kuma ya kara tabbatar da abun da yake a fili tun tuni, cewa Amurka ba ta kasa a gwiwa, wajen tsoma baki cikin harkokin gidan sauran kasashen duniya, muddin dai hakan zai ba ta damar cimma burin siyasa da ta sanya gaba, duk da sukan da hakan ke sha daga sassan kasa da kasa.

Abun damuwa dai kamar yadda sassan kasashen duniya ke nunawa, shi ne a duk lokacin da Amurka ta shiga harkokin sauran kasashe ta kan haifar da tashe-tashen hankula, da jefa al’ummunsu cikin mawuyacin hali, irin wanda har kullum ke sanya daukacin al’ummar duniya Allah wadai da shi.

LABARAI MASU NASABA

Gwamnatin Sin Ba Ta Taba Bukatar Kamfanoni Su Tattara Ko Adana Bayanai Ba Bisa Ka’ida Ba Kuma Ba Za Ta Yi Hakan Ba 

Adadin Motocin Da Sin Ke Fitarwa Waje Ya Karu Da Kashi 15.7 Cikin Watanni 10 Na Farkon Bana

An ga irin wannan yanayi a kasashe irin su Iraki, da Libya, da Afghanistan, da ma wasu sassan kasar Sin kamar yankin Taiwan da na Hongkong, inda Amurkan ke daukar matakai daban daban na ruwa wutar tashin hankali, da ta da zaune tsaye. Ga kuma rikicin Rasha da Ukraine da a wannan lokaci Amurkan ta zamo “Kanwa uwar gami” wajen wanzar da shi.

A gefe guda kuwa, sassan kasa da kasa ba su da wani buri, wanda ya wuce ganin Amurka ta maida hankali ga damuwar al’ummar duniya, na wanzar da sulhu, da zaman lafiya, da ci gaban bai daya na daukacin bil adama. (Saminu Hassan)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Gwamnatin Sin Ba Ta Taba Bukatar Kamfanoni Su Tattara Ko Adana Bayanai Ba Bisa Ka’ida Ba Kuma Ba Za Ta Yi Hakan Ba 
Daga Birnin Sin

Gwamnatin Sin Ba Ta Taba Bukatar Kamfanoni Su Tattara Ko Adana Bayanai Ba Bisa Ka’ida Ba Kuma Ba Za Ta Yi Hakan Ba 

November 17, 2025
Adadin Motocin Da Sin Ke Fitarwa Waje Ya Karu Da Kashi 15.7 Cikin Watanni 10 Na Farkon Bana
Daga Birnin Sin

Adadin Motocin Da Sin Ke Fitarwa Waje Ya Karu Da Kashi 15.7 Cikin Watanni 10 Na Farkon Bana

November 17, 2025
An Bude Taron Tattaunawa Kan Wayewar Kai Tsakanin Sin Da Kasashen Larabawa Karo Na 11 A Beijing
Daga Birnin Sin

An Bude Taron Tattaunawa Kan Wayewar Kai Tsakanin Sin Da Kasashen Larabawa Karo Na 11 A Beijing

November 17, 2025
Next Post
Yajin Aikin ASUU: Kamata Ya Yi Buhari Ya Fara La’akari Da Rahotan Briggs —Kungiyar Iyaye

Buhari Ya Sha Alwashin Karin Goyon Baya Ga Dakarun Soji A Kokarinsu Na Yaki Da Ta'addanci

LABARAI MASU NASABA

Ana Zargin ’Yan Ta’adda Sun Kashe Janar Ɗin Soji A Harin Kwanton-Ɓauna A Borno

Ana Zargin ’Yan Ta’adda Sun Kashe Janar Ɗin Soji A Harin Kwanton-Ɓauna A Borno

November 18, 2025
Bukatar Samar Da Cikkakken Tsaro Ga Hukumar Zabe

’Yansanda Sun Tura Tawaga Don Ceto Ɗaliban Da Aka Sace A Kebbi

November 18, 2025
Gwamnatin Sin Ba Ta Taba Bukatar Kamfanoni Su Tattara Ko Adana Bayanai Ba Bisa Ka’ida Ba Kuma Ba Za Ta Yi Hakan Ba 

Gwamnatin Sin Ba Ta Taba Bukatar Kamfanoni Su Tattara Ko Adana Bayanai Ba Bisa Ka’ida Ba Kuma Ba Za Ta Yi Hakan Ba 

November 17, 2025
Adadin Motocin Da Sin Ke Fitarwa Waje Ya Karu Da Kashi 15.7 Cikin Watanni 10 Na Farkon Bana

Adadin Motocin Da Sin Ke Fitarwa Waje Ya Karu Da Kashi 15.7 Cikin Watanni 10 Na Farkon Bana

November 17, 2025
Farashin Kayan Abinci Na Cigaba Da Sauka A Jihohin Arewa Maso Gabas

Farashin Kayan Abinci Na Cigaba Da Sauka A Jihohin Arewa Maso Gabas

November 17, 2025
An Bude Taron Tattaunawa Kan Wayewar Kai Tsakanin Sin Da Kasashen Larabawa Karo Na 11 A Beijing

An Bude Taron Tattaunawa Kan Wayewar Kai Tsakanin Sin Da Kasashen Larabawa Karo Na 11 A Beijing

November 17, 2025
NBS

Hauhawar Farashin Kayayyaki A Nijeriya Ta Ragu Zuwa Kashi 16.065%

November 17, 2025
Firaministan Sin Ya Isa Rasha Domin Halartar Taron SCO

Firaministan Sin Ya Isa Rasha Domin Halartar Taron SCO

November 17, 2025
‘Yansanda Sun Tsaurara Tsaron Iyakokin Kano Bayan Hare-haren ‘Yan Bindiga 

‘Yansanda Sun Tsaurara Tsaron Iyakokin Kano Bayan Hare-haren ‘Yan Bindiga 

November 17, 2025
Kudaden Kasafin Kudin Sin Sun Karu Da Kashi 0.8 Cikin Watanni 10 Na Farkon Bana

Kudaden Kasafin Kudin Sin Sun Karu Da Kashi 0.8 Cikin Watanni 10 Na Farkon Bana

November 17, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.