Kungiyar gamayyar biranen dake rajin yada ilimi tsakanin al’umma a duk tsawon rayuwa ko GNLC, karkashin hukumar ba da ilmi da kimiyya da al’adu ta MDD wato UNESCO, ta sanya biranen Nanjing da Suzhou na gabashin kasar Sin, cikin jerin biranen duniya da suka yi fice wajen samarwa al’ummunsu damar kara ilimi a duk tsawon rayuwa.
GNLC mai matsuguni a birnin Paris na kasar Faransa, ta ce biranen biyu na samarwa al’ummunsu zarafin koyo a dukkanin matakai. Sun kuma shiga jerin biranen dake cikin jadawalin ne bayan amincewar gungun kwararru.
- Masana’antar Kera Jiragen Ruwa Ta Sin Ta Samu Karin Riba A Shekarar Bara
- Sin Tana Bunkasa Aikin Gona Tare Da Kyautata Muhallin Halittu
Da take tsokaci kan hakan, babbar daraktar UNESCO Audrey Azoulay, ta ce, birane su ne ginshikin samar da damar ilmantar da al’umma, da sanya mafarkinsu zama gaskiya, musamman ga jama’ar dake da mabambantan shekaru.
Birnin Nanjing, fadar mulkin lardin Jiangsu dake daura da kogin Yangtze, ya shirya fadada tsarinsa na koyar da ilimi na duk tsawon rayuwa a makarantu, da tsarin musamman ga daukacin al’ummarsa nan zuwa shekarar 2035.
A nasa bangare kuwa, birnin Suzhou, wanda ke yamma da birnin Shanghai, na mayar da hankali ne ga samar da daidaito ga kowa a fannin samar da damar neman ilimi, da daidaita damar tsakanin mazauna yankunan birane da na karkara, tare da ingiza samar da kayayyakin koyo da koyarwa, domin gajiyar dukkanin rukunonin al’umma a duk tsawon rayuwa. (Saminu Alhassan)