Khadija Bello matashiya ce da duk da lalurar rashin iya tafiya da ya same tun tana makarantar sakandire hakan bai hana ta cika burinta na samun nasara a harkokin kasuwancin da ta sa a gaba ba. Wakiliyarmu Amina Bello Hamza ta tattauna da ita, inda ta bayyana yadda ta fara sana’ar saka da kuma sayar da atamfa. Ga dai yadda tattaunawar ta kasance.
Da Farko Za Mu So Ki Bayyana Mana Sunanki?
Sunana Khadija Bello, ina zaune garin Samarun Zariya, na yi karatu firamari da sakandari duk a Samarun Zariya.
Ko Malamar Nada Aure?
Ban yi aure ba ina zaune da iyayena ne
Wanne sana’a kike yi a halin yanzu?
Sana’a nake yi a yanzu shi ne sakar kayan sanyi sannan ina sayar da duk wani nau’i na sutura, kamar atamfa takalma, a takaice dai har kayan Lefe na aure muna hadawa
Menene Ya Baki Sha’awar Fara Wannan Sana’ar?
Ni tun da farko na tashi da son inga ina wani abu, saboda ko da yaushe ina zaune sai na nemi wani abu da zan rinka yi wanda zai dauke hankalina daga kan larurar da nake fama da ita (ina fama da lalurar rashin iya tafiya), tun da na tashi na ga mahaifiyata na saka sai nima na fara a hankali tun ban kai shekara goma ba nake sakar, A hankali kuma sai hankalina ya kai kan sutura, naga ina so in fara sai na nemi masu siyarwa suka ban shawara suka kara kwadaitamin har na ji Ina son sana’ar a raina sosai sannan na fara.
Idan Mutum Na Son Fara Wanna Sana’ar, Wani Abu Zai Tanada Don Samun Cikakkiyar Nasara?
Idan saka ne zaka tanaji kwarasshe da zare sannan ka mayar da hankali domin shi sakar yana son natsuwa, ta yadda in an nuna maka yau gobe za ta iya kwatantawa
Idan Kuma sayar da sutura ne kamar ni gaskiya nafi siyarwa a kafafen sadarwa na zamani ‘Social Media’ toh za ta bukaci wayar daukar hoto, sannan lokaci ta yadda idan me son siyan kaya ya yi magana za ta iya samun cikakken lokacin da za su yi ciniki har a kai ga aika musu da kayan.
Ta yaya kike tallata hajojinki?
Kinga ni Facebook na fi tallata hajata sai Whatsapp, idan zan yi tallar kayan nakan sa garin da nake sannan na sa number na ta yadda duk me bukata zai min magana inbod a Facebook (Deejah bint Bello) ko a kira number ta 0808403680 ko su yi min magana ta Whatsapp a number da na rubuta.
Ko kin taba samun tallafin gwamnati ko wata hukumar a harkar kasuwancinki?
Ban taba samu ba amma inda zan samu wani tallafi inaso, sai in bude babban shago in dauki ma’aikata wadanda za su ringa tayani kula da shagon, Ta yadda su ma za su samu abin yi.
Ko zaki bayyana mana wani abin da ya taba faruwa da ke na farin ciki ko akasin haka a rayuwarki na wannan sana’ar?
Farin ciki kullum, alhamdulillah, amma akwai kayan lefen da na fara hadawa a rayuwata, ranar na yi farin ciki sosai domin abin da ban yi tsammani ba ne, kwatsam kuma sai ya zo gareni shi yasa har yau na kasa mantawa, na bakin ciki kam bawai babu ba ne, amma farin cikin yana danne shi, Alhamdulillah.
Wanne shawara kike da shi ga al’umma?
Shawarana shi ne su yi hakuri yanzu rayuwa ta yi tsada ba komi ake samu yadda ake so ba, sai an yi hakuri an jure za a ji dadi nan gaba, Duk wanda yake da damar karatu to su yi iya kokari suga sun yi karatunnan sosai, idan kuma sana’ar ne toh kar a sa sanya a yi sana’ar da gaske, Da yawa sukan kasa jurewa a kan abin da suke kai wasu kuma suna da gaggawa, suna so su fara yau kuma har a sansu a yau, a a hakan ba zai yiwu ba sai an yi hakuri an tafi a hankali.
Ya kike ganin yanayin tarbiya a wannan lokacin?
Tarbiyya yanzu sai iyaye sun dage da sa ido sannan su dage da addua duk wuya iyaye su yi kokari wajen sauke hakkin da ya hau kansu, A kula da karatunsu idan babu halin karatu a samu a koya musu sana’a domin rashin abin yi shi ne ke haifar da tabarbarewar tarbiyya idan yaro ba karatu ba abin yi hakan zai sa zuciyarsa ta gurbace har ta kaishi ga aikata wani abu mara kyau wadda iyaye ba za su ji dadi.
Ko kina da wani shawara ga al’umma?
Mu ci gaba da hakuri sannan in mun samu da sauki mu saukaka wa al’umm hakan zai kawo mana sauki da sauyi a rayuwarmu gaba daya, Allah yasa mu da ce.