Sahihancin Kungiyar Gamayyar Jam’iyyun Siyasar Nijeriya:
Mafi akasarin ‘yan Nijeriya, sun dawo daga rakiyar siyasa; domin kuwa fagen a halin yanzu ya zama na wadanda suka kware a fagen cin amana da rashin gaskiya da yaudara da cuta da kuma makirci. Haka nan, su ma jam’iyyun siyasa suna fifita son kai fiye da son Nijeriyar da kuma halin da ‘yan kasa ke ciki. Yayin da su kuma mabiya da sauran ’yan kasa suka samu kansu a cikin wani irin yanayi, sakamakon yin watsi da aka yi da al’amuransu ta hanyar ko-in-kula da halin da suke ciki.
A cikin wannan yanayi na rudanin siyasa, Nijeriya ta tsinci kanta a cikin yanayin da ya yi kama da teku; inda igiyar ruwa ke girgiza ta tare da jan ta, da alama kuma tana kara nitsewa cikin tekun baharmaliyar demokaradiyya.
Saboda haka, a wannan hali da ake ciki; ‘yan Nijeriya na matukar bukatar jirgin ruwan da za su shiga ya kai su tudun mun tsira, kwatsam a cikin wannan yanayi na hadari sai ga jirgin ruwan ‘Inter-Party Adbisory Council’ IPAC, (Gamayyar Jam’iyyun Siyasun Nijeriya).
Abin tambaya a nan shi ne, shin anya wannan jirgin zai iya kai ‘yan Nijeriya tudun mun tsira ko kuwa bai zai iya tseratar da su daga ruwan da ya yi kama da ruwan dufanan wannan demokaradiyya? Wannan na nuni da cewa, IPAC da alama ta samu kanta cikin wani mawuyacin hali yanzu.
Har ila yau, makasudin kafa IPAC shi ne, don samar da kyakkyawan yanayin hadin kai tsakani jam’iyyun siyasa a Nijeriya, inda kuma za ta samar da daidaito tare da bayar da dama ta hanyar da jam’iyyun siyasar za su samu filin bayar da tasu gudunmawar wajen ci gaban Nijeriya. A hannu guda kuma, ta samar da mafita ga ‘yan Nijeriya, sakamakon yadda aka dade ana gasa musu aya a hannu.
Amma kash! A aikace IPAC ta kasa cimma wannan buri wajen ciyar da siyasar Nijeriyar gaba, inda ta zama abin tausayi tare da zama kamar ‘yar Mowa.
Tambaya Mai Muhimmanci Mai Kuma Bukatar Amsa:
Shin IPAC za ta iya ciyar da demokaradiyyar Nijeriya gaba tare da samar mata da mafita ko kuwa ta zamo wani abu ne daban; wanda manyan jam’ iyyu ke amfani da ita wajen cimma burikansu a siyasance?
Darajar IPAC: Shin Fitila Ce Mai Haske A Cikin Hazo?
Shin mai ya faru da IPAC? Amsar tana cikin gazawar sanin muhimmancin hadin kai da kuma tafiyar bai- daya a aikace. IPAC ya kamata ta zama mai kara kuzari wajen gwagwarmayar samun canji, ba kawai dakin babban taron tattaunawa ba, sannan kuma ya kamata ta zama wata inuwa wadda ‘yan Nijeriyan da ba su da uwa a bakin murhu; za su iya zuwa su samu mafita. A cikin wannan rudani IPAC ta rasa wata turba mai daraja a wajen ‘yan Nijeriya.
Duk da halin da a ke ciki yanzu, ka da mu yanke kauna daga samun sa’ida, domin kuwa akwai wata dama da za a iya samun canji, amma idan an samu canjin fahimta a cikin kungiyar IPAC din, an kuma samu yardar cewa Nijeriya ita ce gaba, ba san rai ko fifita wata jam’iyya ba. Wannan kuwa zai samu ne kadai idan:
- Akwai Hadin Kai: IPAC a matsayin lema ga dukkanin jam’iyyun siyasu a Nijeriya, ya kamata ta zama wani wurin na hadin gwiwa, wanda duk jam’Ãyyu za su zama tsaran juna ba abokan gaba ba.
- An Samu Canji Mai Ma’ana:
IPAC ya kamata ta zama wani dandamali; wanda jam’iyyun siyasa za su samu damar bayar da tasu gudunmawar wajen ci gaban siyasa a Nijeriya .
- Akwai Hadin Gwiwa Da Taimakekeniya:
Haka nan, ya kamata IPAC ta zama ‘tsintsiya madauri daya’ , idan jam’iyyu za su samu fagen taimakekeniya a tsakaninsu tare da yin tasiri a fagen siyasar Nijeriya, ko shakka babu, za ta zama kamar wani hasken wuta mai yi wa jiragen ruwa jagora zuwa bakin teku.
- Ginshikin Adalci:
Ya kamata IPAC ta zama wani waje ne, wanda ‘yan siyasa za su samu horo; ta yadda adalci da rikon amana zai rika wanzuwa.
Tsara Sabon Tattakin Siyasa A Nijeriya
Babu shakka, lokaci ya yi da ‘yan siyasar Nijeriya za su yi karatun ta-nutsu, su kuma rungumi harkar siyasa da hannu biyu, inda gaskiya da rikon amana da sadaukar da kai zai kasance a matsayin gaba; ba yin magudi ko ha’inci ba.
Har ila yau, wajibi ne mu kwana da sanin cewa, hakkin duk dan Nijeriya ne bayar da tasa gudunmawar wajen ci gaban kasa da kuma ‘yan kasa. Haka nan kuma, yanzu ya zama wajibi masu madafun iko da zababbun ‘yan majalisa, su kasance masu bayar da bayanai tare da ba’asi bisa alkawarurrukan zabe da suka yi da kuma daukar alhaki na kin cika wanna alkawarurruka da suka yi.
Haka zalika, wannan tafiya ta kowane dan Nijeriya ce, wanda ke fatan ganin wayewar gari mai cike da walwala da jindadi.
A karshe, ci gaban demokaradiyya ba hawan manyan motoci ba ne, ko gina manyan gidaje ko wawure dokiyar kasa ba, ci gaban siyasa shi ne samun ingantaciyar rayuwar ‘yan kasa cikin aminci da daraja. Yanzu lokaci ya yi da Nijeriya za ta samu shugabanni jajirtatttu, wadanda kasar ce a zuciyarsu ba kawai abin da za su samu ba. Sannan, su kuma ‘yan kasa wajibi ne su zama masu yin zabe bisa akida ba don dan abin da za a ba su ba.
Alhaji Adamu Rabiu ya ruwaito da ga Kaduna