• English
  • Business News
Saturday, July 19, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Xi Jinping Ya Aike Da Sakon Murnar Bude Taron Kolin AU

by CGTN Hausa
1 year ago
in Daga Birnin Sin
0
Xi Jinping Ya Aike Da Sakon Murnar Bude Taron Kolin AU
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Labarai Masu Nasaba

Philippines Na Zama Tushen Tashin Hankali A Tekun Kudancin Kasar Sin

Kasar Sin Ta Gano Ma’adanin Yuraniyom Mafi Daraja A Karkashin Kasa Mai Zurfi

Yau Asabar 17 ga wata ne shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aike da sakon taya murnar bude taron kolin kungiyar tarayyar Afirka AU karo na 37.

A sakon nasa, shugaba Xi ya ce, a halin yanzu, ana fuskantar manyan sauye-sauye a duniya, kuma kasashe masu tasowa, ciki har da kasar Sin da kasashen Afrirka na kara bunkasa, abun dake haifar da babban tasiri ga ci gaban duniya.

  • Wang Yi: Kamata Ya Yi Sin Da Birtaniya Su Bunkasa Musaya Da Hadin Gwiwa

Ya ce AU tana himmatuwa wajen hada kan kasashen Afirka, da kokarin dunkule duk nahiyar baki daya, tare da gina yankin cinikayya maras shinge.

Kasar Sin ta kuma taya AU murnar shiga cikin kungiyar G20, abun da a cewarta, zai kara wakilci, da karfin fada-a-ji na kasashen Afirka a harkokin dukkanin duniya.
Shugaba Xi ya kuma jaddada cewa, a shekarar da ta gabata, dangantakar Sin da Afirka ta bunkasa yadda ya kamata, kuma an yi nasarar gudanar da shawarwari tsakanin shugabannin Sin da na Afirka, inda suka kudiri aniyar goya wa juna baya wajen lalubo hanyoyin zamanantar da kansu, da kirkiro yanayi mai kyau ga cimma muradunsu.
A shekara ta 2024, za’a gudanar da taron FOCAC a sabon zagaye, wato taron dandalin tattauna hadin-kan Sin da Afirka, kuma shugaba Xi ya sha alwashin yin kokari tare da takwarorinsa na kasashen Afirka, wajen samar da alfanu ga al’ummunsu, da tsara sabuwar taswirar hadin-gwiwar Sin da Afirka, gami da kara gina al’ummu masu kyakkyawar makoma ta bai daya. (Murtala Zhang)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: AfirkaAUgeneral assemblySummitTaroXi Jinping
ShareTweetSendShare
Previous Post

IPAC: Tasiri Ko Rashin Tasirinta A Siyasar Nijeriya

Next Post

Yadda Tarbiyar Da ‘Ya’yan Da Iyayensu Suka Rabu Ke Shiga Garari

Related

Philippines Na Zama Tushen Tashin Hankali A Tekun Kudancin Kasar Sin
Daga Birnin Sin

Philippines Na Zama Tushen Tashin Hankali A Tekun Kudancin Kasar Sin

8 hours ago
Kasar Sin Ta Gano Ma’adanin Yuraniyom Mafi Daraja A Karkashin Kasa Mai Zurfi
Daga Birnin Sin

Kasar Sin Ta Gano Ma’adanin Yuraniyom Mafi Daraja A Karkashin Kasa Mai Zurfi

9 hours ago
Yawan Jarin Waje Da Sin Ta Samu Ya Haura Dalar Amurka Biliyan 700
Daga Birnin Sin

Yawan Jarin Waje Da Sin Ta Samu Ya Haura Dalar Amurka Biliyan 700

10 hours ago
Sin Ta Yi Allah Wadai Da Hare-Haren Da Isra’ila Ta Kai Syria
Daga Birnin Sin

Sin Ta Yi Allah Wadai Da Hare-Haren Da Isra’ila Ta Kai Syria

11 hours ago
Hanya Mai Salon Musamman Da Kasar Sin Take Bi Wajen Raya Harkokin Kudi
Daga Birnin Sin

Hanya Mai Salon Musamman Da Kasar Sin Take Bi Wajen Raya Harkokin Kudi

12 hours ago
Peng Liyuan Ta Halarci Bikin Hada Hannun Matasa Da Yaran Sin Da Amurka Na Shekarar 2025
Daga Birnin Sin

Peng Liyuan Ta Halarci Bikin Hada Hannun Matasa Da Yaran Sin Da Amurka Na Shekarar 2025

22 hours ago
Next Post
Yadda Tarbiyar Da ‘Ya’yan Da Iyayensu Suka Rabu Ke Shiga Garari

Yadda Tarbiyar Da 'Ya'yan Da Iyayensu Suka Rabu Ke Shiga Garari

LABARAI MASU NASABA

Dangote

Dalilin Da Ya Sa Dangote Ya Jinjina Wa Hukumar NPA

July 18, 2025
Philippines Na Zama Tushen Tashin Hankali A Tekun Kudancin Kasar Sin

Philippines Na Zama Tushen Tashin Hankali A Tekun Kudancin Kasar Sin

July 18, 2025
2027: Atiku, Obi Da Amaechi Za Su Rattaba Hannu Kan Yarjejeniyar Takarar Shugaban Kasa A ADC

2027: Atiku, Obi Da Amaechi Za Su Rattaba Hannu Kan Yarjejeniyar Takarar Shugaban Kasa A ADC

July 18, 2025
Kasar Sin Ta Gano Ma’adanin Yuraniyom Mafi Daraja A Karkashin Kasa Mai Zurfi

Kasar Sin Ta Gano Ma’adanin Yuraniyom Mafi Daraja A Karkashin Kasa Mai Zurfi

July 18, 2025
majalisar kasa

Kirkirar Sabbin Jihohi Da Kananan Hukumomi Sun Dabaibaye Sauraron Jin Ra’ayoyin Gyaran Tsarin Mulki

July 18, 2025
Ƙwallon Mata: Nijeriya Ta Lallasa Zambia Da Ci 5-0

Ƙwallon Mata: Nijeriya Ta Lallasa Zambia Da Ci 5-0

July 18, 2025
Yawan Jarin Waje Da Sin Ta Samu Ya Haura Dalar Amurka Biliyan 700

Yawan Jarin Waje Da Sin Ta Samu Ya Haura Dalar Amurka Biliyan 700

July 18, 2025
A Karon Farko Dino Melaye Ya Bayyana A Gaban Kotu A Matsayin Lauya

A Karon Farko Dino Melaye Ya Bayyana A Gaban Kotu A Matsayin Lauya

July 18, 2025
Biyan Tukuici: Gwamna Yusuf Ya Ƙaddamar Da Tallafin Naira 50,000 Ga Mata 5,200 Duk Wata A Kano

Biyan ‘Yan Fansho Naira Biliyan 22: NUP Da NLC Sun Bukaci A Yi Koyi Da Gwamna Abba

July 18, 2025
Sin Ta Yi Allah Wadai Da Hare-Haren Da Isra’ila Ta Kai Syria

Sin Ta Yi Allah Wadai Da Hare-Haren Da Isra’ila Ta Kai Syria

July 18, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.