Shafin TASKIRA, shafi ne da yake zakulo muku batutuwa daban-daban wadanda suka shafi al’umma, ciki sun hadar da; zamantakewar aure, rayuwar matasa, rayuwar yau da kullum, soyayya, da dai sauransu. Tsokacinmu na yau zai yi duba ne game da, yadda tarbiyyar wasu yara ke gudana musamman wadanda iyayensu suka samu rabuwar aure tsakani. Inda shafin ya ji ta bakin wasu daga cikin ma’abota shafin TASKIRA game da wannan batu; Ko yaya makoman yaran ke kasancewa bayan iyayensu sun rabu da juna?, Yaya tarbiyyarsu ke gudana?, ta wacce hanya za a shawo kan matsalar dake afkuwa ga ‘ya’ya?. Ga dai bayanan nasu kamar haka:
Sunana Aminu Adamu, Malam Madori A Jahar Jigawa
To magana ta gaskiya wannan matsala tana shafar rayuwar yaran sosai domin yaran basa samun cikakkiyar kulawar tarbiyya da ma sauran abubuwan rayuwa wanda hakan ke jawo su tashi cikin kuncin rayuwa, a lokuta da dama idan ba a yi sa’a ba rayuwar ta lalace su taso munanan dabi’u wanda za su zama matsala ga al’umma baki daya. To hanya ta farko dai ya kamata iyayen su fifita masalahar ‘ya’yansu akan ta su masalahar don haka su yi hakuri da juna muddin akwai sauran igiyar aure a tsakaninsu a maida wannan aure domin inganta rayuwar yaransu, hanya ta biyu kuma idan auren ba zai gyaru ba ya kamata uban ya tabbar ya auri matar da za ta iya rike masa yaran tsakani da Allah ba wai mai fuska biyu ba. To shawarar dai ita ce da farko su yi hakuri da juna muddun akwai sauran igiyar aurensu a maida auren domin inganta rayuwar yaransu, idan kuma zaman aure ya kare a tsakaninsu to uban dole ya dauki matakin neman mace ta gari wadda za ta rike masa yaran tsakani da Allah, domin wasu matan suna yin fuska biyu suna azabtar da yaran ba tare da uban ya gane ba, daga karshe nake addu’ar Allah ya kawo mana karshen wannan matsala a kasar Hausa.
Sunana Balkisu Musa Galadanchi, Daga Jihar Sokoto Nigeria:
A mafi akasarin rabuwar auren da ke zuwa da ‘ya’ya a tsakaninsu yaran sun fi kowa cutuwa saboda daga wannan ranar sun fara gararamba kenan, tarbiyyar yaran za ta fara tangal-tangal saboda babu majingina guda. Hakuri da juna muddin aka yi aure har aka tara zuri’a to mafi a’ala shi ne a yi hakuri da rabuwar indai ba dalilin rabuwar ya kai matakin abinbda addini ya ce a yi saki dominsa ba, shi dinma wanda ba za a iya hakura a yi don Allah ba. Tsayuwa tsayin daka wurin inganta tarbiyar yaran koda basa tare da su, yawan yi musu nasiha da jansu a jiki a san me duniyarsu take ciki kada a yi sakaci da addu’a saboda goben yaran.
Sunana Iliya Mustapha Umar Bakin Zuwo (Iliya India), Daga Jihar Kano:
To, a zahirin gaskiya kalma guda daya ce duk ita take haifar da wani abu ita ce; rashin hakuri. Inda jama’a za su yi hakuri daga mazan har matan to, duk da ba za ta kai da wannan matsayin da yaranmu ke tsintar kansu ciki ba, rashin hakuri shi zai sa mace ta kasa wadatywa da abin da miji zai bata, shi kuma daga gurin miji nasa rashin hakurin shi zai janyo cewar abu kalilan shi ma ba zai iya hakuri da shi ba, dukka sai a taru kowa ya hau kan dokin zuciya a nuna fushi. To! a yayin da aka samu rabuwa kuma ta kasance da yara tsakani babu abin tausayi face wadannan yaran. Na farko dai tun daga tarbiyyarsu, karatunsu, hatta da daukar nauyinsu, sautari za a ga cewar mace ta fita ko da ciki ko kuma da kananan yara sai a samu cewar shi uban duk wani hakki da yake kansa na yaron nan ya yi buris ba kowanne me tsoron Allah bane yake iya daukar nauyin yaran da, uwa ta fita da su ko kuma ta fita da ciki. Wani idan ya dan yi sai ki ga wani sai an je Hisbah ko kuma sai an je kotu, sannan zai yanka abin da zai dan rinka bayarwa wanda abin na tabbata ba isa zai yi ba. To har gara ace maraici ne mutuwa ce ta raba, za a ga masu tausayi suna kawo gudunmawa dan kula da wadannan yaran koda daga cikin bangaren dangin uwar ne, amma yayin da ake ganin cewar ga ubansu to, kowa zai kauda kai ne ba zai yi ba, tunaninsa ai ubansu yana nan yana yi, ita kuma uwa ita kadai ta san halin da take ciki, uban yana yi-baya yi Allahu ya’alamu. Amma duk wani abu uwa za ta yi kokarin yi wa ‘ya’yantai, abu daya ne yake yi wa uwa nauyi shi ne; daukar nauyin karatu, sau tari za a ga irin wadannan yaran idan har ba ubansu bane ya dau nauyin makaranta ba to uwa fa in ba wata me gwaggwabar sana’a ba, ba ta iya wa, wannan dalili ke sa yaran tun daga wannan lokacin sun taso sun fara bin yaran banza, abokai na banza na unguwa, karshe kuma sai tarbiyya ta lalace. Saboda haka idan da za a dawo kan kalmata ta farko a yi hakuri da zamantakewa duk inda aka kai tsadar rayuwa kowa hakuri ake daidai ruwa daidai kurji, iya abin da za ka iya, iya ita ma tayi hakuri kai kayi hakuri sai a zauna lafiya. Mu rayu da yaranmu, mu ruke abinmu, mu tarbiyyartar da su, har Allah ya kawo lokacin da su ma za su girma su yi nasu iyalin, wannan shi ne a takaice, Wassalam.
Sunana Hafsat Sa’eed, Daga Jihar Niger:
Makomar ‘ya’ya ya danganta, wani lokacin daga uba wani lokacin kuma daga matan uba, wasu kuma koda suna tare uwa ita ke kokari akan ‘ya’yanta musamman akan karatu, to idan ta rabu da mijin ta bar ‘ya’ya suna tsintar kansu cikin rashin tarbiyya in mace ce sai a ga ta shiga biye-biyen maza ko shaye-shaye in namiji ne kuwa sai a ga ya zama dan iska, ko dan shaye-shaye ko barawo. Shawo matsalar kuwa shi ne uwa ta ja danta ko ‘yar ta don uwa tafi kula da ‘ya’yanta fiye da uba ta dawo dasu gareta ta basu tarbiyya me kyau. Shawarata ga iyaye anan shi ne in hakan ya kasance kar a yi fishi abar yara a gidan ubansu in ma ba yadda za ta yi to ta kasance koda yaushe tana kai musu ziyara tana jansu a jiki ko ita tana iya bibiyar tarbiyyarsu koda bata gidan.
Sunana Hassan Muhammad, Wuriwa Hadejia Jihar Jigawa:
A zahirin gaskiya mafi yawan lokuta tarbiyyar ‘ya’ya kan tabarbare yayinda aka samu rabuwa a tsakaninsu, musamman idan a kace yara ne kanana da basu kai nauyin iya daukar dawainiyar kansu da kansu ba hakan na iya zama silar bata gari, za ka ga sun shiga rayuwar su hakanne kansa wasu lokuta ka ga an samu yawaitar yi wa kananan yara fyade. Ya zama dole Al’umma su sanya hannu wajen kula da tarbiyyar yaran dake rayuwa a kusa dasu, ba sai lalle nasu yaran ba. Ya zama wajibi iyaye kada su bari rabuwar aurensu ya shafi tarbiyyar yaransu ta fuskar tuntubar juna kan rayuwar yaran tsakanin matar da kuma mijin.
Sunana Sadiya Garba (S Girl), Daga Jihar Kano:
Eh! to, idan har aka bar yara a hannun mahaifi gaskiya suna samun matsala wajen tarbiyyar su, saboda shi namiji ba mazauni bane ita kuma wadda ya aura ba lallai ta tsaya ta kula da tarbiyyar su ba, saboda mu mata munada mugunta akan abin da ba namu ba. Hanya daya ce idan har saki ya afku tsakaninku to lallai ki tafi da yaranki indai basu mallaki hankalinsu ba. Shawarar da zan bawa iyaye mata shi ne idan har hakan ya afku to koda yaran suna hannun mahaifinsu lallai suna bibiyar rayuwar yaran nan, su saka ido sosai akansu saboda yanayin rayuwa, kuma su dage saka su cikin addu’o’insu domin wannan zamanin ko a gaban ka yara suke sai ka hada da addu’a dole.
Sunana Mansur Usman Sufi (Sarkin Marubutan Yaki), Daga Jihar Kano Najeriya:
Rabuwar aure tsakanin mata da miji gaskiya babbar damuwa ce dake taba makomar tarbiyyar yara sosai, domin sau tari sukan bar hannun iyayensu mata, a kai su zuwa gidan dangin miji, wanda idan ba a yi da gaske ba tarbiyyar tana samun rauni. Hanyar da za a magance hakan shi ne uba ya zamo nagari ya auri ‘ya da iyayenta suka kasance na kwarai, haka ita ma a bangaren macen, domin duk lokacin da rabuwar aure ta gifta dayansu ba zai damu ba don an aika yaronsa wani gida ya zauna domin samun tarbiyya. Shawara daya ce iyaye da rabuwar aure ta faru tsakaninsu kar su bari hakan ya shafi yaransu, ta kowacce fuska, Allah ya sa mu dace Amin.
Sunana Hadiza Ibrahim Ɗ. Auta Ƙaura-Namoda Jihar Zamfara:
A kan samu kaddarar rabuwar aure ga ma’aurata. Idan an samu irin wannan matsala yaran da ke tsakaninsu suna shiga wata irin rayuwa tamkar marayu. Musamman idan an raba su da mahaifiyarsu an mika su hannun matar uba. Saboda rashin kulawar da za su fuskanta a hannunta idan aka yi rashin dace kuma ta jefa rayuwarsu cikin mawuyacin hali. Domin koda a hannun mahaifiyarsu suke matukar basu tare da shi a kusa za su kasance cikin kewar mahaifinsu a wasu lokutan, koda ba su rasa komai ba. Babbar hanyar shawo matsalar ita ce; tsakanin matar uban da aka bar wa su, ko kuma shi mahaifinsu da ya raba su da mahaifiyarsu; ko kuma ita uwar ta rike yaranta a hannunta gudun kada su yi kukan babu; dukansu ya dace su ji tsoron Allah su san duk abin da ya faru ga yaran suna da laifi a wurin Allah. Sannan bugu da kari; wasu mazan suna bar wa mace ragamar yaran duka idan an rabu. Saboda bahagon tunanin da suke yi wai ita suka yi wa don su bata haushi. Bayan sun manta da cewa mari ne tare da tsinka jaka matukar aka saketa kuma aka barta da hidimar yaran akwai cutarwa. Don wani da gangan yake yin hakan saboda kawai ta tagayyara rayuwarta ta shiga matsala a garin nemo abin da yaran za su ci da sauran matsalolin rayuwa. A wautarsa ita ce yayi wa bai san kansa ya cuta ba, domin idan ya rike su rikon da ya dace duk da ya rabu da mahaifiyarsu ba za su kasa ganin girmansa ba. Amma muddin ya yi watsi da su bayan ya gama tozarta musu uwa; wallahi ko ba a fada ba kowa ya san ba za su taba ganin girmansa ba koda an kai lokacin da zai kasa ba za su tallafa masa ba matukar zuciyarsu ta kekashe da jin haushin rikon sakainar kashin da ya yi musu a lokacin da suke bukatar agajinsa. Shawarar da zan bayar a kan wannan matsala; su yi aiki tukuru a kowane bangaren matar da mijin duka koda sun rabu, domin su tallafi yaransu duk inda zamansu ya fi karkata. Kada mace ta ce ba za ta taimaki yaranta ba wai don suna hannun mahaifinsu. Domin komai yake yi musu akwai bukatar ta jefa tata kulawa ta jiki da aljihunta domin gudun su fada wata muguwar rayuwa saboda rashin tata kulawa. Shi ma mijin koda yaran ba su hannunsa yana da kyau ya zame musu bango da za su jingina su ji sanyi. Saboda shi ne ubansu kuma wanda ba suda wani sai shi a duniya. Fadansa da uwarsu har abada ba zai goge matsayinsa a wurinsu ba, sai dai yakan lalata alakar ta yi rauni matukar ya ce zai bar mata ragamarsu shi ya tankwashe hannu. Domin fushin zuciyar da zai yi ta bangaren rashin kulawarsa gare su; yana iya haifar da wata kiyayya tsakanin yaran da shi. Saboda bai kula da su a lokacin da suka fi bukatar hakan ba, domin ko suna da abinci, sutura da muhallin zama a wurin mahaifiyarsu; a gefe daya kuma suna neman kusancinsa gare su domin ya debe musu kewar da za su raba bambanci da marayun da nasu uban ya mutu. Saboda akwai wanda na sani tun da ya rabu da matarsa har zuwa dogon lokaci bai nemi yaran ko a waya ya ji lafiyarsu ba. A tunaninsa don ya rabu da uwarsu su ma ba su da wani amfani a wurinsa. Don haka ina kira da ubanni masu irin wannan halin da su ji tsoron Allah. Su tuna hakkin yaransu a lokacin da suke kanana ya fi girma da nasa hakkin da ke kansu a lokacin da suka mallaki hankalin kansu. Kada su jefar da yaransu kuma su yi tunanin idan yara sun girma za su ji kansu.