Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Abuja (AEDC) ya baiwa cibiyoyin gwamnati 86 da suka hada da fadar shugaban kasa (Villa), Ma’aikatu da Hukumomin gwamnati wa’adin kwanaki 10 na su biya bashin sama da Naira biliyan 47 da ake binsu ko kuma a yanke musu wutar lantarkin.
Cikin jerin wadanda ake bin bashin akwai barikin babban hafsan hafsoshin tsaro da ake bin bashin fiye da naira biliyan 12, ma’aikatar babban birnin tarayya, biliyan 7.5, ma’aikatar kudi, naira biliyan 5.4 sai kuma Ofishin Hulda da Jama’a na Jihar Neja da ke Abuja, Naira biliyan 3.4.
Sauran sun hada da: Ma’aikatar Albarkatun Man Fetur, Fadar Shugaban Kasa, Ma’aikatar Ilimi, Gwamnan Babban Bankin Nijeriya, Rundunar ‘Yansandan Nijeriya, da dai sauransu.