A wata sanarwa da gwamnatin jihar Kano ta fitar ta hannun Kwamishina yada labarun jihar, Baba Halilu Dantiye, ta musanta zargin da ake yadawa a kafafen yada labaru daban-daban dangane da sakin Murja Ibrahim Kunya – fitacciyar ‘yar TikTok daga Gidan gyaran hali.
A cewar sanarwar, gwamnatin Jihar Kano bata da wata masaniya ko wani yunkuri na sa hannu ko baki dan ganin ta shiga Shari’ar ko kuma wani yunkuri makamancin haka.
- Za Mu Yi Wa ‘Yan TikTok Auren Gata – Hisba
- Rundunar ‘Yansandan Jihar Kano Ta Cafke Jarumar TikTok Murja Ibrahim Kunya
Sanarwar tace, gwamnatin Abba Kabir Yusuf na yin iya kokarinta ganin ta bar kowanne bangare na gwamnati wajen aiwatar da aiyukansu ba tare da yin katsalandan a ciki ba.
Tun bayan samun labarin fitar Murjar daga Gidan gyaran hali, Labaru da dama sun karade shafukan sada zumunta, inda wasu ke zargin Gwamnatin Kano da Hukumar Gidan gyaran hali da Hukumomin Shari’a na jihar da katsalandan kan fitarta daga Gidan amma duk sun musanta zargin.