Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya yi tir da karairayin da ake yadawa game da kisan kiyashi da kuma tilastawa mutane yin aiki a jihar Xinjiang, sannan ya yi kira da a yi kokarin kauce wa ra’ayin “tabka hasara” a yayin da yake amsa tambayoyi a taron tsaro na Munich a ranar Asabar.
Wang Yi ya ce, tun lokacin da aka kafa yankin Xinjiang na kabilar Uygur mai cin gashin kansa, yawan mutanen Uygur ya karu daga miliyan 3 zuwa sama da miliyan 12 ya zuwa yanzu. Kuma ana ba da kariya ga ‘yancin gudanar da addini na dukkan kabilu da ke wurin, inda ya ba da misali da cewa musulmai na da isasshen wuraren ibada kuma gwamnati ta dauki nauyin gyara da kula da masallatai.
- Wang Yi: Sin Ta Sha Alwashin Zama Jigon Samar Da Daidaito A Duniya Mai Tangal-Tangal
- Xi Ya Jaddada Bukatar Kara Amfani Da Filaye Don Bunkasuwar Yankuna Mai Inganci
Da yake magana game da zargin da ake yi cewa ana tilastawa mutane yin aiki, Wang ya ce, yin amfani da wannan zargi a matsayin uzuri don shafawa kasar Sin bakin fenti, wata manufa ce ta kwace wa al’ummar Uygur ayyukan yi tare da hana su sayar da hajojinsu.
Ya kara da cewa, ci gaban da kasar Sin ta samu cikin sauri ya haifar da rashin jin dadi da damuwa a tsakanin mahukuntan wasu kasashe, shi ya sa suke yada karairayi game da jihar Xinjiang don haifar da cikas, ta yadda za a hana ci gaban kasar Sin da farfado da tattalin arzikinta.
Bugu da kari, Wang Yi ya ce, ra’ayin da wasu ke da shi na “tabka hasara”, ba zabi ne da hankali zai dauka ba, kuma cin nasara tare shi ne makomar dan Adam.
Rahoton na shekara-shekara da aka fitar a Litinin din nan gabanin kammala taron tsaro na Munich, ya jaddada damuwar da ake da ita kan ra’ayin “tabka hasara”, yayin da ake samun karuwar tashe-tashen hankula a fannin siyasa da karuwar rashin tabbas na tattalin arziki.
A cewar rahoton, gwamnatoci da dama ba sa mai da hankali kan cikakkiyar fa’idar hadin gwiwar duniya, maimakon haka suna kara nuna damuwa cewa, suna samun moriya kasa da ta saura.
Wang ya ce, rahoton ya nuna yadda nahiyar Turai ke tunani da kuma damuwar da duniya ke ciki.
Ya bayyana cewa, bangaren kasar Sin ya yi imanin cewa, ra’ayin cin moriya da faduwar wani, da neman bayar da wasu saniyar ware, da yunkurin yin fito-na-fito na wani gungu ne ke haifar da ra’ayin “tabka hasara”. Yana mai cewa, kasashe da yawa sun fahimci cewa, tilas ne a kaucewa hasara.
Ya kara da cewa, ya kamata mu yi aiki tare, mu yi la’akari da muradun wasu tare da kare muradun kanmu, da inganta ci gaban hadin gwiwa tare da neman ci gaban kanmu, ta yadda za mu samu nasara tare, kuma nasara shi ne burin da ya kamata mu bi tare.
Wang ya ce, idan har ana son cimma nasara tare, kamata ya yi kasashe su zabi hadin kai kan rarrabuwar kawuna, hadin gwiwa kan sabani da bude kofa ga juna.
A ranar 18 ga watan Fabrairu ne aka kammala taron kwanaki uku na taron tsaro na Munich karo na 60 a birnin Munich na kasar Jamus. A yayin taron, mahalarta daga kasashe daban-daban sun tattauna batutuwa kamar rikicin Ukraine, rikicin Isra’ila da Falasdinu da kuma tsarin kasa da kasa. (Masu Fassarawa: Muhammed Yahaya, Ibrahim Yaya)