Gwamnatin jihar Kano ta kaddamar da kwamitin shirin ciyar da abincin watan Ramadan na shekarar 2024 a fadin jihar.
Da yake kaddamar da kwamitin a ranar Laraba a Kano, mataimakin gwamnan jihar, Aminu Abdussalam, ya ce, an kaddamar da shirin ne domin taimakawa mazauna jihar ba tare da la’akari da banbancin siyasa ba.
- Gwamna Dikko Umar Ya Taya Kwamarad Dan Ali Murnar Zama Shugaban NUJ Mafi Kwazo A Arewa Maso Yamma.
- Gwamnatin Tarayya Za Ta Kaddamar Da Shirin Tallafawa Magidanta Miliyan 12
Ya bukaci kwamitin da su tsara dabarun raba kayan abinci a yankunan da aka kebe a jihar, tare da bayyana muhimmancin kammala aikinsu cikin kwanaki biyar.
Lokacin azumin Ramadan, mai kwanaki 29 ko 30 na azumin a tsakanin al’ummar Musulmin duniya, za a fara ne nan da kwanaki 18 masu zuwa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp