Wata matsala da ke kunno kai tare da yin barazana ga harkokin noma a halin yanzu ita ce, batun mayar da gonaki zuwa filaye ko gidajen kwana a kafatanin jihohin Arewacin wannan kasa baki-daya.
Har ila yau, wannan dalili ne ya sa wakilanmu daga wasu jihohi na Arewacin kasar, suka tattara mana rahotanni ta hanyar tattaunawa da wadanda abin ya shafa, domin kokarin lalubo bakin zaren; ta hanyar jin alfanu da kuma rashin alfanu na wannan dambarwa, inda wasu suka goyi bayan mayar da filayen gonaki, wasu kuma suka soki yin hakan.
- Amurka Ta Zama Babban Cikas Ga Dakile Yakin Gaza Bayan Da Ta Hau Kujerar Na Ki
- Blinken: Idan Ba Ka Da Karfi, Za A Cinye Ka
Ga dai rahotannin da wakilan namu suka aiko mana da su:
Kano
Batun sayar da gonakin noman abinci, musamman ga masu karamin karfin da suke noma dan wani abu daga cikin abincin da suke amfani da shi a gidajensu, yanzu haka ana iya cewa; ana neman mayar da bara bana, domin kuwa halin da gonakin Kano ke ciki; ya zama abin takaici kwarai da gaske.
A shekarun baya, ‘yar gayaunar bayan gida kan iya samar da wasu nau’ikan abinci, wadanda suke daukar lokaci ana amfani da su, kama daga kan wake, kayan miya da kuma dawar tuwo, amma yanzu sakamakon yadda birane suke kara mamaye gonaki da kuma yadda dillalan filaye suka samu sabuwar sana’a, ta yadda masu hannu da shuni ke saye maka-makan gonaki tare da mayar da su filaye; ta hanyar daidai kudinka daidai shagalinka.
Har ila yau, karancin gonakin noman abinci; ba karamar barazana ce ga harkar samar da abinci ga al’ummar Jihar Kano ba, musamman idan aka dubi yadda wasu manyan kamfanonin kasashen waje ke saye ire-iren wadannan gonaki tare da katange su, an hana manoma yin noma; sannan da sunan da aka sayi gonar na cewa za a yi, jama’a su samu aikin yi; shi ma ba a yi ba.
Idan ka bi hanyar Kano zuwa Wudil, Wudil Zuwa Kwanar Garko, haka nan titin Hadeja; takanin Gunduwawa zuwa Jogana, babu wasu sauran gonakin noma, sai manyan katangu da masu kudi suka saye suka killace.
Neja
Dangane da wannan dambarwa, wakilinmu na Jihar Neja ya tattauna da wani mai saye da sayarwa a kan harkar filaye da gidaje, Malam Lawal Yaro; wanda ya bayyana cewa magana ta gaskiya illar sayar da gonaki ya fi alfanunsa yawa.
Domin kuwa a cewar tasa, za ka tarar da iyali guda suna da gonar da ta kai girman hekta sama da hamsin, wanda dukkanin su suka dogara a kanta, amma da zarar wata baraka ta taso a tsakanin su, sai su sayar wa da mutum daya, wanda shi zai noma ba, ba kuma zai ba wa wani ya yi noman ba.
Haka zalika, matsalar tsaro ta hana mutune zuwa dazuka wadanda ke da nisa, wanda kuma in dai har mutum manomi ne na gaskiya, ya fada cikin irin wannan jarabawa; dole ne ya koma makwafta don neman rufin asiri kamar yadda take faruwa a tsakanin Nufawa da Gwarawa a wannan lokaci.
Dalili kuwa shi ne, abin takaici ne ka tashi daga Minna zuwa Bidda ka ga filayen gonaki an killace su ba a yin noman kwata-kwata, kuma ba a ba wa wasu su yi noman ba.
Haka zalika, wannan tsadar abinci da ake fama da ita; ta biyo bayan rashin samun damar noma wadataccen abinci ne tare da sayar da gonakin da ake yi ga ‘yan kasuwa, wasu na yanka filayen suna sayarwa, wasu kuma suna killace su ba tare da yin komai a wurin ba.
Nassarawa
Har ila yau, daga Jihar Nassarawa; wakilinmu ya samu tattaunawa da wasu daga cikin manoma, dangane da alfanu da kuma rashin alfanun mayar da gonaki filaye.
Alhaji Abubakar Danjuma, guda ne daga cikin manoman jihar wanda ya bayyana cewa, a shekarun baya ba a samun matsalar abinci, musamman abin da ya shafi bangaren kayan miya sakamakon cewa akwai wadatattun filaye a kusa da gari.
A wannan lokaci, mutane suna noma abin da za su ci a gida, idan kayan miya ne kuma ga lambu a kusa da gida; sai dai kawai a je a debo a kawo, amma yanzu komai ya yi wahala sakamakon babu lambun noman tumatur ko Alaiyahu da sauran makamantansu. Ya kara da cewa, kamata ya yi idan aka yanka nan ya koma gidaje, sai kuma a bude wani wurin daban.
A bangare guda kuma, Mista Asile Manga ya bayyana nasa ra’ayin, inda ya bayyana cewa; yanzu mutane sun yi yawa a wannan kasa. Saboda haka, wajibi ne kowa ya nemi matsugunin da zai zauna da iyalinsa.
Don haka, dole ne a yanka gonakin da ke kusa da gari, duk da dai kuma bai kamata a rika sare bishiyoyin da ke kusa da su ba. Domin kuwa, barin itace yana da matukar amfani.
Kaduna
Masana harkokin gidaje a Nijeriya, sun bayyana irin karancin matsalar gidaje da ake samu a wannan kasa, wanda yawansu ya kai kimanin miliyan 22; duk da kokarin gwamanatoci ke yi na dukufa wajen mayar da gonaki zuwa gidaje.
Har ila yau, masanan bayyana cewa; kashi 80 cikin 100 na ‘yan Nijeriya, ba sa iya gina gida ko fitar da kudi su saya. Kazalika, matsalar na kara munana da karancin gidaje 900,000 a kowace shekara.
A Jihar Kaduna, mafi yawan gonakin da ake yin noma; yanzu sun fara komawa birane, lamarin da wasu suke ganin akwai alfanun mayar da gonakin zuwa gidaje, wasu kuma ke ganin hakan ba shi da wani alfanu.
A kokarin da ‘yan kasuwa ke ci gaba da yi na mayar da gonaki zuwa filaye a halin yanzu, ya sa Gwamnatin Jihar Kaduna kirkirar sabbin birane; domin fadada birnin Kaduna, ta hanyar mayar da gonaki zuwa gidajen zama.
Mutane da dama na ci gaba da kokawa dangane da yadda ake mamayar gonakinsu ana mayar da su gidaje, koda-yake wasu kuma na ganin yin hakan na da matukar alfanun gaske.
Alhaji Shafi’u Salisu Abubakar, Shugaban Kungiyar Dillalan Gidaje da Filaye ta Jihar Kaduna ya bayyana cewa, akwai alfanu mai tarin yawan gaske wajen mayar da gonaki birane.
Ya kara da cewa, duk da yadda ake mayar da gonaki gidaje har yanzu ana samun karancin gidajen zama ga al’umma, wanda wannan ba karamar babbar barazana ba ce.
“A nan Jihar Kaduna, idan ka dauki Dan Bushiya da Dan Huni da Keke da dai sauran sabbin wurare, duk sun zama kananan birane; wanda a shekaru goma baya duk daji ne wurin ko da kudi aka ce ka shiga, ba za ka iya shiga ba; amma yanzu wurin ya koma kamar kana Abuja.
Saboda haka, ko shakka babu akwai alfanu mai yawan gaske; idan aka mayar da gonaki zuwa birane. Sannan kuma, ai yin hakan ba zai hana a yi noman ba, domin kuwa har yanzu muna da sauran wuraren yin wannan noma masu yawan gaske a fadin wannan jiha,” in ji shi.
Katsina
Daga Jihar Katsina, wakilinmu ya tattauna tare da jin ta bakin wadanda ke da ruwa da tsaki, kan wannan dambarwa, Alhaji Hassan Tsagem; guda ne daga cikin ‘yan kasuwa masu sayen gonaki suna mayar da su filaye; domin sayarwa jama’a, wanda ya dauki tsawon lokaci yana wannan sana’a.
Har ilayau, Tsagem kara da cewa; amfanin mayar da gonaki filaye na da matukar muhimmanci, musamman a wurinsu ‘yan kasuwa sana’a mai matukar kyau a gare su, na biyu kuma hanya ce ta saukaka wa masu karamin karfi, domin mallakar filaye samakon cewa, a irin wannan lokaci mutane ba za su iya sayen gidaje a mayan unguwanni ko sayen fili awon gwamnati ba.
“A duk yayin da muka sayi gona, wanda dama mafiyawan gonakin a wajen gari suke, sai mu yanka su zuwa filaye tare da sayar da su ga talakawa masu karamin karfi.
Gaskiyar magana shi ne, babu wani mutumin kauye da ke son rabuwa da abin da ya gada iyaye da kakannin, idan har ba ya zama dole ba, domin wani lokacin idan ba ka sayar ba; za a yi maka barazanar kwace wurin, hakan ya sa ake sayarwa don samun kwanciyar hankali, a cewar ta Kalla.
Jigawa
Dangane da sauya gonakin noma zuwa filaye, a Jihar Jigawa ma dai ba ta sauya zani ba, domin kuwa al’ummar jihar kullum na ci gaba da kokawa.
Alhaji Ahmad Rufa’i, manomi ne kuma mazaunin Birnin Dutse, ya bayyana lamarin a matsayin wani babban kalubale, wanda ke jefa dubban matasa cikin wani yanayi na rashin aikin yi tare da zaman kashe wando.
Kazalika ya bayyana cewa, duk da kasancewar mafi yawan gonakin, gwamnati na amfani da su wajen gina ma’aikatu da gidajen ma’aikata, wanda ko shakka babu shi ma wani ci gaba ne, amma hakan na kara barazanar karancin samun abinci.
Shi kuwa a nasa bangaren, wani dillalin filaye mai suna Alhaji Mu’azu, ya bayyana wannan lamari a matsayin ci gaba musamman ga manyan birane a jihar ta Jigawa.
Mu’azu ya kara da cewa, a duk inda ka ga ana sauya gonaki zuwa filaye; babu wani abu a wannan wuri illa ci gaba ga al’ummar da ke zaune a yankin.
“Wadansu gonakin an mayar da su masana’antu, wanda hakan ya bai wa matasa damar samun ayyukan yi tare da bunkasa tattalin arzikinsu. Sannan, dukkanin wani birni; yana bunkasa ne sakamakon amfani da gonakin da ake yi zuwa gine-gine da kuma kawata shi.
Kebbi
Jihar Kebbi, na daya daga cikin Jihohin Nijeriya wadanda suka yi suna wajen noma da samar da abinci, amma a halin yanzu ita ma na fama da matsalar yanka gonaki ana mayar da da su filaye, don gina gidajen kwana.
Ko shakka babu, wannan matsala da ke kunno kai; za ta yi matukar jawo karancin samar da abinci ga jihohin kasar nan, musamman Jihar Kebbi da ta yi kaurin suna wajen noma abinci a fadin Nijeriya baki-daya.
A wata tattaunawa da wakilinmu ya yi da wani tsohon ma’aikacin ma’aikatar filaye da gina gidaje, wanda ya nemi a sakaye sunansa ya bayyana cewa, “Matsalar mayar da gonaki filaye don gina gidaje, ba karamar matsala ba ce; domin kuwa za a kai ga lokacin da ba za a iya samar da abinci a jihohinmu na Nijeriya ba. Don haka, ya zama wajibi ga gwamnatotin jihohi da tarayya su farga don samar da mafita.
Shi ma wani manomi mai suna Audu Bello Birnin Kebbi ya bayyyana cewa, a shekaru goma da suka gabata yana da gonakin noman abinci dai-dai har guda tara wadanda ya gada daga wurin mahaifinsa, amma sakamakon wannan matsala ta mayar da gonaki zuwa filaye, ta sa ya rabu da guda takwas saura daya kacal a halin yanzu.