• English
  • Business News
Saturday, November 1, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Rikita-rikitar ‘Yar Tiktok Murja Kunya Da Hukumar Hisba A Kano

by Abdullahi Muh'd Sheka
2 years ago
Hisba

A cikin makon nan ne  labarin fitar shararriyar ‘yar Tik-Tok dinnan wadda ake zargi da yawan kalaman batsa da rashin sanin ya kamata ta shiga hannun jami’an Hisbaar JIhar Kano bayan kwashe tsawon lokaci ana farautarta Bayan samun nasarar damke ta  ne kuma hukumar HIsba ta gurfanar da ita gaban kotun shari’ar musulunchi dake Kwana Hudu a yankin Karamar Hukumar Nasarawa inda kotun ta aike da ita gidan gyaran halin na Kurmawa har zuwa ranar 20 ga wtan feburairin shekara ta 2024 domin ci gaba da sauraron karar.

A cikin dakon zuwan wannan rana da kotu ta ayyana domin ci gaba da sauraron karar ta Murja Ibrahim Kunya, sai kwatsam labarin fitar ta daga gidan gyaran halin ya fantsama akafafen sada zumunta, wanda haka ya haifan da zafafan martini tare da zargin hannu wasu masu mulki ko masu hannu da shuni da ake ganin sune suka yi duk mai yiwuwa wajen satar hanyar fitar da Murjar, sannan kuma aka ci gaba da cece ku ce a kafafen sada zumuntar wanda hakan ne ya ja hankalin bangarorin daban daban da ake kallo suna da ruwa da tsaki cikin lamarin.

  • Firaministan Sin Ya Jagoranci Taron Majalisar Gudanarwar Kasar 
  • Zaben Fitar Da Gwani Na APC A Edo Ya Bar Baya Da Kura

Tunda farko hukumar lura da gidajen gyaran hali na Jihar Kano ta bakin mai Magana da yawunta Musbahu Kofar Nasarawa Hukumar kula da gidajen ta musanta rahotanni cewa fitacciyar ‘yar Tik tok  Murja Ibrahim Kunya ta gudu daga gidan yari.

Musbahu K/Nasarawa cewa ya yi Wasu rahotanni  sun karade kafafen sada zumunta dake cewa Murja Kunya  wadda kotu ta aike da ita gidan ajiya ranar Larabar da ta gabata bisa zargin ta da ayyukan badala da bata tarbiyya a kafafen sada zumunta ta tsere daga gidan gyaran halin.

Ta cikin wani sakon murya da ya aikawa kafafen yada labarai, mai magana da yawun hukumar Musbahu Lawal Kofar Nasarawa, ya ce an saki Murja bisa beli kamar yadda doka ta tanada bayan samun takarda daga alkali.

LABARAI MASU NASABA

Trump Ya Ayyana Nijeriya A Matsayin Ƙasar Da Rayuwar Kiristoci Ke Cikin Hatsari

An Tsare Wani Mutum A Gidan Yari Kan Zargin Kashe Matarsa Saboda Ƙuli-Ƙuli A Kano

Ya kara da cewa yamadidin da ake cewar ta gudu daga Gidan gyaran Halin  umarnin harbi ne akan duk wanda aka samu da  laifin guduwa daga gidan gyaran hali, kuma takarda ce ta tsare Murja sannan takarda ce ta sake ta. Inji Musbahu Gwamnatin Kano

An jawo hankalin gwamnatin jihar Kano kan zargin karya da ake ta yadawa a cikin al’umma musamman a kafafen sada zumunta na zamani  kan zargin sakin wata fitacciyar ‘yar TikTok mai suna Murja Ibrahim Kunya daga gidan gyaran hali bisa yada abun da bai dace ba cikin bidiyo sabanin tanadin dokokin da suka dace a  Jihar Kano.

A sanarwar da Kwamishinan yada labarai na Jihar Kano, Baba Halilu Dantiye ya sanyawa hannu, yace Wannan zarge-zargen kwata-kwata ba su da tushe balle makama, ba gaskiya ba ne, rashin sanin ya kamata ne  kuma hasashe na wasu bata-gari da  masu rashin  kishin kasa da kishin Gwamnati da mutuncin Gwamnan Jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf.

Idan dai ba a manta ba gwamnati ta san Murja Kunya ta gurfana a gaban wata Kotun Shari’a da ke Kwana Hudu a karamar Hukumar Nassarawa bisa zargin ta da yada wasu munanan faifan bidiyo a dandalin sada zumunta inda kotu ta bayar da umarnin tsare ta a gidan  gyaran hali kuma zuwa ranar Talata, 20 ga Fabrairu, 2023 bayan ta saurari bukatar neman belin ta. Sai dai ya zo ma Gwamnati cewa an sake samun wani sabon zarge-zargen da aka yi mata wanda ya sa jami’an tsaro suka fitar da ita domin bincike. Har yanzu dai shari’arta na ci gaba da wanzuwa kuma za ta ci gaba har zuwa matakin karshe da kotu ta yanke.

Don haka ana kira ga jama’a da su yi watsi da zargin da ake yi wa Gwamnatin jihar Kano a matsayin ba komai bane illa kokarin bata mata suna  tare da tabbatar wa al’ummar jihar cewa za ta ci gaba da mutuntawa tare da kiyaye alfarmar abubuwan da aka tanadar a kundin tsarin mulkin tarayyar Nijeriya. Inji Dantiye

A Halin yanzu haka Talatar Nan ne aka sake gabatar da Murja gaban kotu, Kuma tunda farar Safiya ita Murja ta halrci kotun, Kuma alkalin ya tambayi lauyanta inda ta amsa da cewar Yana hanya, Amma dai kotun tace ba zata jira zuwan lauyan nata ba, saboda haka sai kotun ta bada umarnin ga ma’aikatar Lafiya da akai Murja Asibitin domin bincika Kwakwalwar ta sannan ta bukaci Hukumar Hisba data ci gaba kulawa duk waniotsin Murja Ibrahim inda ta dage sauraron Shari’ar ta ta zuwa 20/5/2024.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Donald Trump Zai Gurfana A Gaban Kotu Kan Tuhumar Da Ake Masa
Manyan Labarai

Trump Ya Ayyana Nijeriya A Matsayin Ƙasar Da Rayuwar Kiristoci Ke Cikin Hatsari

October 31, 2025
Yadda Waliyin Amarya Ya Sace Sadaki A Kano
Manyan Labarai

An Tsare Wani Mutum A Gidan Yari Kan Zargin Kashe Matarsa Saboda Ƙuli-Ƙuli A Kano

October 31, 2025
Gwamna Uba Sani Ya Gabatar Da Kudirorin Raya Jihar Kaduna A Taron Ƙoli Na Biranen Asiya A Dubai 
Labarai

Gwamna Uba Sani Ya Gabatar Da Kudirorin Raya Jihar Kaduna A Taron Ƙoli Na Biranen Asiya A Dubai 

October 31, 2025
Next Post
An Cafke Motocin Dako 50 Makare Da Abinci Za Su Shiga Nijar A Zamfara

An Cafke Motocin Dako 50 Makare Da Abinci Za Su Shiga Nijar A Zamfara

LABARAI MASU NASABA

CMG Ta Kammala Gabatar Da Rahoto Kan Ganawar Shugabannin Sin Da Amurka

CMG Ta Kammala Gabatar Da Rahoto Kan Ganawar Shugabannin Sin Da Amurka

October 31, 2025
Ministan Wajen Malawi: Tsarin Ci Gaban Kasar Sin Ya Samar Da Darussa Ga Kasashe Masu Tasowa

Ministan Wajen Malawi: Tsarin Ci Gaban Kasar Sin Ya Samar Da Darussa Ga Kasashe Masu Tasowa

October 31, 2025
Xi: A Shirye Sin Take Ta Hada Hannu Da Canada Wajen Mayar Da Dangantakarsu Bisa Turbar Da Ta Dace

Xi: A Shirye Sin Take Ta Hada Hannu Da Canada Wajen Mayar Da Dangantakarsu Bisa Turbar Da Ta Dace

October 31, 2025
Donald Trump Zai Gurfana A Gaban Kotu Kan Tuhumar Da Ake Masa

Trump Ya Ayyana Nijeriya A Matsayin Ƙasar Da Rayuwar Kiristoci Ke Cikin Hatsari

October 31, 2025
Yadda Waliyin Amarya Ya Sace Sadaki A Kano

An Tsare Wani Mutum A Gidan Yari Kan Zargin Kashe Matarsa Saboda Ƙuli-Ƙuli A Kano

October 31, 2025
Xi Ya Gabatar Da Rubutaccen Jawabi Ga Taron Kolin Shugabannin Masana’antu Da Kasuwanci Na APEC

Xi Ya Gabatar Da Rubutaccen Jawabi Ga Taron Kolin Shugabannin Masana’antu Da Kasuwanci Na APEC

October 31, 2025
Gwamna Uba Sani Ya Gabatar Da Kudirorin Raya Jihar Kaduna A Taron Ƙoli Na Biranen Asiya A Dubai 

Gwamna Uba Sani Ya Gabatar Da Kudirorin Raya Jihar Kaduna A Taron Ƙoli Na Biranen Asiya A Dubai 

October 31, 2025
Ya Kamata Sin Da Amurka Su Zama Kawayen Juna Ba Abokan Gaba Ba

Ya Kamata Sin Da Amurka Su Zama Kawayen Juna Ba Abokan Gaba Ba

October 31, 2025
Zaben 2027 Zai Kasance Ne Tsakanin Mulkin Tinubu Da Zabin Ƴan Nijeriya —Atiku Abubakar

Zaben 2027 Zai Kasance Ne Tsakanin Mulkin Tinubu Da Zabin Ƴan Nijeriya —Atiku Abubakar

October 31, 2025
Makarantar Kogi Poly Ta Bankaɗo Masu Ƙirƙirar Takardun Kammala Karatu na Bogi

Makarantar Kogi Poly Ta Bankaɗo Masu Ƙirƙirar Takardun Kammala Karatu na Bogi

October 31, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.