Bayyanar jirgin saman fasinja samfurin C919 kirar kasar Sin, a bikin nuna jiragen sama na shekarar 2024 a kasar Singapore, ya samu yabo daga sassa daban daban, a matsayin babban ci gaban fannin kere-keren hajoji na Sin. Ana danganta wannan ci gaba da yadda fannonin bunkasar tattalin arzikin Sin ke samun karin tagomashi.
Kuri’un jin ra’ayin al’umma na kasa da kasa da kafar CGTN, da hadin gwiwar jami’ar Renmin karkashin cibiyar bincike ta kasa da kasa ta “New Era”, sun nuna kaso 87.1 bisa dari na wadanda suka bayyana ra’ayin su, sun yaba da kwazon kasar Sin a fannin bunkasa ingancin tattalin arzikinta ta hanyar kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha, da amincewa da sabon tsarin samar da hajoji masu inganci, matakin da zai taimakawa wayewar kan kasar Sin, ta yadda zai zamo cikin sauri da nagarta.
Zamanantarwar kasar Sin, sabon tsarin ci gaba ne ba tare da gurbata muhalli ba, wanda hakan jigo ne na raya tattalin arzikin kasar na samar da ci gaba mai inganci.
kuri’un jin ra’ayin al’ummar ya kuma nuna cewa, kaso 91.9 bisa dari sun nuna gamsuwa ga manufofin Sin na girmamawa, da kare muhallin al’umma a tafarkinta na zamanantar da kai, kana sun jinjinawa kokarin Sin na yunkurin wanzar da kyakkyawan yanayin zaman jituwa tsakanin bil adama da muhallan dake kewaye da shi.
Yayin kuri’un jin ra’ayin al’ummar, an tuntubi mutane 11,180 daga sassan duniya daban daban, ciki har da na kasashe masu wadata kamar Amurka, da Birtaniya, da Faransa, da Sifaniya da Australia, da kuma na kasashe masu tasowa, kamar Brazil, da Thailand, da hadaddiyar daular Larabawa, da Masar da Afirka ta kudu. (Mai fassara: Saminu Alhassan)