• English
  • Business News
Wednesday, October 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwamna Dauda Ya Sanar Da Ɗaukar Ma’aikata Da Samar Da Garejin Tireloli A Zamfara

byLeadership Hausa
2 years ago
zamfara

Gwamna Dauda Lawal na Jihar Zamfara, ya amshi rahotannin ayyuka daban-daban da gwannatinsa ke aiwatarwa a duk faɗin jihar a yayin taron Majalisar zartarwar jihar a ranar Litinin a zauren majalisar da ke gidan gwamnati a Gusau.

Mai magana da yawun Gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya ffitar da sanarwar cewa majalisar zartarwar ta zauna a karo na 16 tun hawan gwamnatin Gwamna Dauda Lawal.

A cewarsa, shugaban majalisar, Gwamna Lawal, ya samu cikakkun rahotanni kan ci gaban da aka samu, da ƙalubalen da aka fuskanta, da kuma lokacin da ake sa ran kammala kowane aiki.

Waɗannan ayyuka da ake gudanarwa sun shafi sassa daban-daban, gami da ababen more rayuwa, kiwon lafiya, ilimi, da tilasta bin doka.

  • Tsadar Rayuwa: Sojoji Sun Ƙaryata Jita-jitar Shirin Yi Wa Shugaba Tinubu Juyin Mulki

LABARAI MASU NASABA

ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

A yayin jawabin da ya yi wa majalisar, Gwamna Lawal ya jaddada muhimmancin ‘aikin ceto Zamfara’ na gwamnatinsa, wanda ya ba da fifiko wajen tabbatar da gaskiya da riƙon amana.

“Muna da babban nauyi a gabanmu yayin da muka fara aikin ceto. Burin mu shi ne cetowa, tare da sake gina Zamfara, kasancewar ba mu da wani wurin da za mu kira gida sai nan.

“Na amince da ɗaukar ma’aikata 250 aiki a Hukumar Kula da Zirga-zirgar Ababen Hawa ta Zamfara (ZAROTA) nan take domin inganta ayyukan gine-ginen da gwamnatina ke gudanarwa a cikin birane.

“Na umurci kwamishinan shari’a da babban lauyan gwamnati da su kafa kotun da za ta kula da laifukan da suka shafi ababen hawa.

“Bugu da ƙari, za mu samar da wurare na manyan motoci guda biyu a Gusau domin daƙile cunkoson ababen hawa da tireloli ke haddasawa.”

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki
Labarai

ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

October 8, 2025
Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu
Labarai

Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

October 8, 2025
Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung
Manyan Labarai

Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

October 8, 2025
Next Post
Rana Ba Ta Karya: Habakar Tattalin Arzikin Kasar Sin Ya Ba Mahassada Kunya

Rana Ba Ta Karya: Habakar Tattalin Arzikin Kasar Sin Ya Ba Mahassada Kunya

LABARAI MASU NASABA

Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

October 8, 2025
ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

October 8, 2025
Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

October 8, 2025
Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

October 8, 2025
A Kama Wani Likitan Bogi A Neja

‘Yansanda Sun Kama Masu Laifi 153, Sun Ƙwato Miyagun Ƙwayoyi A Jihar Jigawa

October 8, 2025
An Fara Biyan Ma’aikata Sabon Mafi Ƙarancin Albashin N70,000 A Borno

‘Yansanda Da Mutanen Gari Sun Daƙile Harin Boko Haram A Borno

October 8, 2025
…ACF Ta Nesanta Kanta Da Goyon Bayan Akpabio

‘Yan Nijeriya Sama Da Miliyan 33 Ne Ke Fama Da Matsananciyar Yunwa – Akpabio

October 8, 2025
Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

October 7, 2025
Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

October 7, 2025
Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

October 7, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Go to mobile version