A safiyar yau Talata ne ma’aikatan gwamnatin tarayya karkashin kungiyar ‘yan kwadago ta Nijeriya (NLC), suka yi dandazon jama’a a fadin jihohin kasar nan, domin fara zanga-zanga ta kwanaki biyu a fadin kasar, dangane da tabarbarewar tattalin arziki da tsadar rayuwa a kasar.
A makon da ya gabata ne dai kungiyar NLC ta kasa ta fitar da sanarwar wata zanga-zanga ta kwanaki biyu da za a yi a fadin kasar a ranakun 27 da 28 ga watan Fabrairu kan tsadar rayuwa da ‘yan Nijeriya ke fuskanta musamman ma’aikata sakamakon rashin tsaro da cire tallafin man fetur da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta yi.
- Rundunar Sojoji Ta Karrama Jami’anta 10 Bisa Ƙwarewa A Yaƙi Da Ta’addanci
- Majalisar Zamfara Ta Dakatar Da Mambobi 8 Tare Da Rusa Kwamitocinta
Shugaban kungiyar ta NLC, Joe Ajaero, ne ya jagoranci ma’aikatan a wata zanga-zangar da aka fara a hedikwatar kungiyar da ke Abuja, inda za ta kare a harabar majalisar dokokin kasar.
Har ila yau, wakilanmu sun ba da rahoton bin umarnin NLC a jihohin Legas, Kuroa Ribas, Ebonyi, Gombe, Oyo, Ondo, Kogi da Ribas, da dai sauran jihohi inda ma’aikata suka yi tattaki kan tituna domin nuna damuwarsu kan halin da ake ciki na ‘yunwa, talauci da rashin tsaro’.
Rundunar ‘yan sandan Nijeriya a fadin Jihohin kasar ta yi alkawarin samar da tsaro ga masu zanga-zangar lumana da sauran masu bin doka da oda a yayin zanga-zangar kamar yadda ta gargadi masu tayar da kayar baya.