Gwamnatin Jihar Zamfara bisa jagorancin Gwamna Dauda Lawal za ta gina sabuwar Tashar Motocin Tilera guda biyu a Gusau Babban Birnin Jihar.
Dauda ya bayyana haka a wani a taro da ya gudanar a ranar Talata a gidan gwamnati da ke Gusau lokacin da yake karbar bakuncin shugabanin Kungiyar NATO da Kungiyar PTD ta masu dakon man fetur.
- Gwamna Dauda Ya Sanar Da Ɗaukar Ma’aikata Da Samar Da Garejin Tireloli A Zamfara
- Mun Hana Kai Wa ‘Yan Bindiga Burodi Ba Hana Sayarwa Ko Gasawa Ba – Dauda
Lawan ya tattaun da su a kan shirinsa na gina tashar motoci a Titin Funtua zuwa Zariya da kuma Titin Gusau Zuwa Sokoto babban birnin jihar Zamfara.
Babban mataimaki na musamman kan yada labarai na gwamnan, Sulaiman Bala Idris ne ya bayyana haka a wata takarda da yasanya wa hannu.
Da yake jawabi ga mambobin kungiyoyin biyu, Gwamna Lawal ya ce, shirin zai kai inganta hanyoyi a babban birnin jihar.
“Na ba bayar da umarnin gina wuraren Tasha Tirela a kofofin Gusau guda biyu: daya a kan titin Funtua zuwa Gusau daya kuma a kan titin Sokoto zuwa Gusau, ” Cewar Gwamna.