Ana sa ran yawan al’ummar duniya ya kai biliyan 8 a ranar 15 ga watan Nuwamban wannan shekarar, kamar yadda hasashen da Majalisar Dinkin Duniya ta yi a wannan Litinin ya nuna.
Hasashen ya nuna cewa indiya za ta zarce China a yawan Jama’a a cikin shekarar 2023.
Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres ya ce wannan ci gaba da aka samu a bangaren yawan jama’a, tuni ne a kan hakkin da ya rataya a kan al’ummar duniya wajen kula da muhali da yanayi, sannan kuma lokaci ne na nazari a kan inda aka gaza wajen kulawa da juna.
Hasashen da hukumar kula da tattalin arziki da zamantakewa ta Majalisar Dinkin Duniya ta yi ya nuna cewa a karon farko tun bayan shekarar 1950 yawan al’ummar duniya ba ya karuwa cikin sauri.
Rahoton hasashen ya ce yawan al’ummar duniya na iya kai wa biliyan 8 da rabi a shekarar 2030, da biliyan 9 da miliyan dari 7 a 2050, inda daga nan zai tsaya a inda yake har zuwa karni na 22.
A yayin da kasashe masu tasowa da dama ke bin tsarin takaita haihuwa, fiye da rabin karuwar yawan al’umma zai kasance ne a kasashe maso tasowa 8, wato, Jamhuriyar dimokradiyya Congo, Masar, Habasha, Indiya, Nijeriya, Pakistan, Philippines da Tanzania.