Mai magana da yawun gamayyar kotunan jahar Kano Baba Jibo Ibrahim a wata hira da yayi da manema labarai ya bayyana cewar tun ranar 29 ga watan Agustan shekarar 2022 wata karamar kotu dake Bichi ta bayar da umarnin kamo mawaki Ado Isa Gwanja bayan an shigar mata da kara akan wata waka da yake shirin fitarwa a wancan lokacin.
Baba Jibo Ibrahim ya kara da cewar a wancan lokacin mawakin ya garzaya wata babbar kotu a jahar Kano domin ta bashi kariya daga abinda ya kira bata suna da yake zargin ana shirin yi masa.
- Akwai Hannun Gwamnan Kano Wajen Fitar Da Murja Kunya Daga Gidan Gyaran Hali – Jaafar Jaafar
- Mahaifiyar Murja Kunya Ta Koka Kan Ƙoƙarin Yi Wa ‘Yarta Allurar Mahaukata
Hakan yasa babbar kotun a wancan lokacin ta dakatar da umarnin da karamar kotun ta bayar na kamo Ado Gwanja,wanda hakan yasa ya cigaba da gudanar da al’amuran shi cikin lumana ba tareda wata tsangwama ko tashin hankali ba.
A wancan lokacin wata kungiyar malamai ta hannun wasu kwararrun lauyoyi ne ta shigar da Gwanja kara akan wata waka da yake shirin fitarwa wadda ake hasashen zata iya lalata tarbiyar mutane musamman kananan yara.
Da ake tambayar mai magana da yawun gamayyar kotunan sharia na jahar Kano Baba Jibo Ibrahim akan ko wannan umarnin kamun yanada wata alaka da siyasa,sai ya buda baki yace ko kusa bashida alaka da siyasa domin kuwa shekaru biyu da suka gabata maganar take gaban kotu sai a wannan lokacin ne aka bayar da umarni kamoshi domin gudanar da bincike yadda ya kamata.