Gwamnatin Kano ta warware jita-jitar da ke zagayawa bisa rashin kai gaisuwar Sallar mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero a fadar gidan gwamnan jihar lokacin hawan Nasarawa a ranar Litinin, wanda yana cikin al’adar bukukuwan sallar wannan shekara.
Kwimishinan Ma’aikatar Yada Labaran Jihar Kano, Malam Muhammad Garba ne ya sanar da hakikanin yadda lamarin yake, inda ya ce, Gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje na halartar wani taron gaggawa kan wasu muhimman batutuwan kasa a Abuja tare da sauran Gwamnonin a ranar Litinin.
Ya ce gwamnan ya halarci sallar idi tare da Sarkin Kano a filin idi na Kofar Mata, sannan ya tari sarkin a gidan Shettima, sannan kuma ya halarci hawan Daushe da aka gudanar a fadar Sarkin Kano a ranar Lahadi da yamma kafin tafiyarsa Abuja da yamma domin haduwa da sauran gwamnonin.
Malam Muhammad Garba ya ci gaba da bayyana cewa, an tsara gwamnan zai yi wa shugaban kasa bayanin sakamakon zaman a washegari.
Kwamishinan ya kara da cewa, sauran mutum biyu da za su iya wakiltar gwamnan domin karbar gaisuwar Sallah ba tare da karya ka’idar al’adar aiki ba su ne Mataimakinsa, Dakta Nasiru YusUf Gawuna da Kakakin Majalisar dokokin Jihar Kano, Honarabul Hamisu Ibrahim Chidari, wadanda dukkaninsu suna kasa Mai tsarki wajen gudanar da aikin Hajjin bana.
Kwimishinan ya nuna cewa, tun kafin ma tafiyarsa, gwamnan ya tattauna da sarkin bisa wannan sabon ci gaban, inda dukkansu suka aminta da janye gaisuwar Sallar, amma Sarkin zai ci gaba da sauran hawa ta dukkan hanyoyin da aka saba bi ciki har da wucewa ta gidan gwamnati.
Garba ya karyata jita-jitar da ake ta yadawa cewar gwamnan ya kaurace wa ziyarar sarkin ne, saboda haka sai ya bukaci jama’a da su yi watsi da wannan labarin da wasu marasa kishi ke yadawa domin Kawo rudani.