Hassan Muhammad Nawad da Hussaini Muhammad Nawad tagwaye ne haifaffun Jihar Kano ne wanda a halin yanzu suka samu damar shiga cikin baje fasahar kere-kere na duniya da ake tunkaho da shi. Tagwayen masu shekaru 14 a duniya sun kirkiri abun dafa abinci da zai ke amfani da man fetur da ruwa da zai samar da wutan da nau’ikan abinci ke bukata na tsawon sama da awanni biyar a lokaci guda.
Murhun dafa abincin na dauke da injin da ke amfani da baturi da zai sarrafa ruwa da fetur domin bayar da wutan dafa abinci.
- ‘Yan Sama Jannatin Sin Sun Kammala Aikin Gyara Na’ura A Wajen Kumbo A Karon Farko
- Buhari Ya Haddasa Wa Nijeriya Koma-baya Na Tsawon Shekara 50 — Fayose
Da ake zantawa da tagwayen sun shaida cewa sun tsara amfani da kwakwalwarsu wajen hada wani abun da zai zama mai amfani kuma ya taimaki al’umma. A cewarsu, sun sha zama su baje tunani daban-daban kowa ya kawo abun da yake gani za su yi ko za su bada tasu gudunmawar a lokacin da suke zuwa kwanciya don yin barci, inda suke irin wannan tunanin, kuma, iyayensu sun yi matukar mara musu baya da shawarori da kuma tarbiyyar da zai taimakesu wajen cimma burin mafarkinsu tare da dafa wa tunaninsu da kuma kokarin maido musu da abun da suke tunani zuwa ga zahiri.
Hassan ya ce tunanin hada murhun dafa abinci na zamani ya zo musu sama da shekara biyar da suka wuce, a lokacin da suke makarantar Firamare.
“Na yi ta tunanin ta yaya ake amfani da iskar gas wajen bayar da wutan da ake dafa abinci, sannan, da tunanin yin wani abu da zai kawo sauki kan amfani wutar lantarki domin samar da wutar ta hanyar amfani da ruwa da fetur. Daga nan ne muka fara kama-kama har muka kawo wannan lokacin a yau.
“Amma, a wannan yanayin, fetur da ruwa ba za su rage wahalar da ake sha. Litar mai zai dauki watanni ba tare da raguwa ba. Kawai za ka canza ne idan ka fahimci ya koma baki da zai dauki kusan shekara 1 kafin yin hakan. Batiri da karamin injin da aka hada za su taimaka wa ruwa da fetur din ne wajen bulbula iskar da zai samar da iska mai konewa da zai bayar da daidai wutar da ake bukata domin dafa abinci,” ya shaida.
Shi ma Hussaini wanda ya yi bayani da cewa, “Shi wannan ruwan da ake hadawa ba zallar ruwa ne ba, ana hadawa ne da alum da kuma gishiri. A cikin akwatin, za ka iya ganin akwai karamin inji da zai ke bayar da iskar da ruwan da fetur za su ke motsawa.”
Hussaini ya kara da cewa, lura da halin matsatsin tattalin arziki da ake fuskanta a fadin kasar nan, don haka ne suka yi tunanin nemo wasu hanyoyin da za su taimaka wajen rage wa jama’a kuncin da ake ciki da kuma bayar da nasu gudunmawar wajen cigaban tattalin arzikin kasar nan.
“Muna son mu kawo wani gagarumin sauyi a cikin matasan arewacin kasar nan. Mun iya fahimtar cewa an bar matasa a bayan baya, kuma fa muna da basira da fikira sosai. Kawai abun da muke nema shi ne wadatar da za mu samu da zai ba mu damar kirkirar ayyukan yi da kuma samar da ababen bukata da saukaka wa al’umma harkokin rayuwa.”
Duk da cewa har yanzu suna makaranta, wanda suke matakin aji SS2 na sakandari, Hassan ya shaida cewar shi da dan uwansa Hussaini sun kuma kirkiri injin feshi mai amfani da cajin wutar lantarki wanda za a yi amfani da shi wajen feshi domin kashe kwari koda kuwa a cikin ruwa suke.
Ya ce, abun feshin zai ke amfani da batirin da za a ke masa cajin wuta ne. Kuma, zai iya aiki na tsawon kwanaki 10 idan aka cikasa da caji.
“Idan ka samu kayan da kake son yin feshi, kawai abun da kake bukata shi ne za a ka yi cajin abun feshinka ka cigaba da amfani da shi. Kuma wannan abun gwanin ban sha’awa kuma zai yi amfani matuka. Shi ne mafi sauki a cikin dukkanin abubuwan da muka hada.”
Tagwayen suka ce, bayan samun nasarar hada murhun dafa abinci da kuma abun feshin maganin kashe kwari, yanzu haka sun dukufa yin aikin su da ke gabansu, wanda a cewarsu shi ne za su hada batiri wanda zai yi aiki wajen bai wa na’urar sanyaya daki ko wuri (AC) kuzarin da yake bukata domin ba sai da wuta ba kafin ya yi amfani a gidajen mutane.
A cewarsu, wannan batiri zai ke bai wa AC abun da yake nema, kuma koda babu wuta AC zai yi aiki da wannan batirin.
“Aikin da muke son yi a nan gaba shi ne na hada Batiri, kuma mun riga ma har mun fara. Baturi ne mai karfin lantarki 12 da zai bai wa AC kuzarin da yake nema da zai bai wa fankoki, firiza, talabijin da sauran abubuwan amfani damar yin aiki a gidaje. Babban aiki ne sosai da muka dunfara amma muna da kwarin guiwar za mu iya kuma za mu yi. Amma a halin yanzu, muna fuskantar wasu ‘yan matsaloli. Wasu daga cikin abubuwan aiki da muke bukata wajen cimma burinmu babu su amma dole mu tsaya har zuwa lokacin da za mu sameshi,” suka shaida.
Baya ga hakan, sun shaida cewar suna da shirye-shiryen kirkirar wasu abubuwa sosai da za su taimaka wajen yin amfani da su a cikin al’umma, sun kara da cewa suna matukar damuwa da yadda jama’a suke shan wahalar gudanar da harkokin rayuwa musamman talakawa, don haka suka dukufa wajen amfani da basirar da Allah ya basu domin kawo sauki da nemo hanyoyin rage matsaloli ga jama’a.
Da suke magana kan muradinsu da fatansu a nan gaba, tagwayen sun ce, suna da burin karanta ilimin fasaha da kwasa-kwasan da suke da alaka da hakan a jami’a da zarar suka kammala karatun sakandari kuma burinsu a wannan gabar shi ne su tafi kasar Turai ko wata kasar da ta cigaba domin samun karin sani, ilimi, gogewa da horon da za su cigaba da cimma burinsu na rayuwa musamman a bangaren kere-kere.
“Muna da manya-manyan shirye-shirye da buri a nan gaba, za mu cigaba da kirkirar abubuwa sosai. Dangane da murhun dafa abinci, za mu sabunta shi mu zamanantar da shi da kara masa kwari. Kuma za mu kirkiri wani da zai ke kasance na da wurin bada wuta da iskar dafa abinci mai wuri biyar ko ma shida domin amfani da shi a gidajen da suke da yawa ko wajajen taruka.
“Babban abun da muke bukata yanzu shi ne goyon baya, gudunmawa da bibiyar da zai kara wa yunkurin azama da kumaji. Muna da muradi a kan abubuwa daban-daban da suka shafi kimiyya. Kuma, mun kasance masu bibiya da kallon matasa irinmu ko ma wadanda suke kasa da mu domin amfani da baiwar da Allah ya musu, a kasashen da suka cigaba. Muna son mu je irin wadannan wuraren domin samun karin horo,” Hussaini ya shaida.
Kazalika, ma ‘yan biyun sun yi kira ga matasa da su shigo a dama da su a harkokin kirkire-kirkire tare da amfani da harkokin fasaha. Sun ce, idan aka yi la’akari da tawakarorinsu da suke wasu kasashe da yadda suke iya amfanar da al’ummarsu, akwai bukatar matasan Nijeriya su shigo a dama da su wajen karawa da takwarorinsu na kasashen waje.
“A duk lokacin da muka ga wani matashi a bangaren fasaha na bada gudunmawarsa a wata kasa, muna samun kwarin guiwa matuka. Muna son mu ga an samu sauyi a wannan bangaren a Afrika. Amma kalubalen da muke fusanta suna da matukar yawa.
“Wasu lokutan ba mu da kayan aiki da muke bukata. Za mu tsara mu jira ko kuma mu watsar da aikin da muka sanya a gaba ko muka fara. Amma muna da yakin gwamnatocinmu za su shigo su taimaka wa matasan da suke da basira domin a amfani baiwar da Allah ya musu. Ta wannan hanyar za mu yaki matsalar rashin ayyukan yi da talauci a tsakanin matasa da ma al’umma.”
Tagwayen sun kuma bukaci matasa da su yi koyi da abun da suke yi wajen ganin sun taimaka wa al’umma. Sannan, sun gode da jinjina wa cibiyar bunkasa fasahar sadarwa wato (CITAD) bisa tallafin da take basu na kayan aiki da kuma nema musu damar samun zuwa dakunan gwaje-gwaje na fasaha daban-daban kan ayyukansu da suke yi.
“CITAD ta taimakemu da wasu kayayyaki da kayan aiki da dama. Kuma sun taimaka mana da samun damar wuraren kara wa juna sani da dama, inda muke zuwa a kowani rana domin yin ayyukanmu. Wannan a zahiri ya taimaka mana matuka da karfafa mana guiwa wajen cimma manufofin da muka sanya a gaba.