Shugaban kasar Saliyo Julius Mada Bio, ya bayyana fatan yin hadin gwiwa a fannin noma tsakanin kasarsa da lardin Hubei na kasar Sin a jiya Asabar bayan da ya ziyarci cibiyar kula da amfanin gona ta kwalejin kimiyyar aikin gona ta Hubei, inda ya samu labarin nasarori da aka samu a fannin noman shinkafa.
Bio, wanda ya kai ziyarar aiki a kasaAn kira taron manema labarai game da zama na biyu na majalisar bada shawarwari kan harkokin siyasar kasar Sin (CPPCC) karo na 14 da yammacin yau Lahadi 3 ga watan Maris, inda kakakin taron, Liu Jieyi ya gabatar wa kafafen yada labaran gida da na waje abubuwan da suka shafi taron, tare da amsa tambayoyi.
- An Yi Bikin Tunawa Da Ranar Mata Ta Kasa Da Kasa A Beijing
- Yadda Ake Kwakil Na Garin Filato Wanda Aka Fi Sani Da Waken Challa
Kakakin ya ce, za’a kaddamar da zama na biyu na majalisar CPPCC karo na 14 da misalin karfe 3 na yammacin gobe Litinin, a babban dakin taron jama’a dake Beijing, wanda za’a rufe shi a safiyar ranar 10 ga watan, inda za’a takaita ayyukan majalisar CPPCC na shekarar da ta gabata, da tsara shirye-shiryen ayyukan bana. Majalisar za kuma ta kara tallata kyawawan al’adunta, da bude sabon babi ga ayyukanta a sabon zamanin da muke ciki.
Yayin da yake amsa tambayoyin ‘yan jaridun gida da waje, Liu Jieyi ya ce, batun tattalin arziki na jawo hankalin membobin majalisar CPPCC sosai, kana daya ne daga cikin muhimman batutuwan da za’a tattauna a kai. A ganin membobin, a shekarar da ta shude, a karkashin jagorancin kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin wanda Xi Jinping shi ne jigonsa, tattalin arzikin kasar ya murmure, kana an yi nasarar cimma babban burin bunkasuwar tattalin arziki da kyautatuwar zaman rayuwar al’umma. A shekarar da muke ciki, CPPCC za ta ci gaba da bada taimako ga raya tattalin arzikin kasa, da gudanar da shawarwari kan muhimman batutuwan tattalin arziki ta hanyoyi daban-daban, da bayar da kyawawan nasihohi, da tattaro ra’ayoyin mutanen bangarori daban-daban, a wani kokari na bayar da gudummawa ga sha’anin samar da ci gaba mai inganci. (Murtala Zhang)
Sin daga ranar 27 ga watan Fabrairu zuwa 2 ga Maris, ya samu lambar yabo ta digirin digirgir a ranar Asabar din daga jami’ar kimiyyar binciken kasa ta kasar Sin (Wuhan).
Da yaka jawabi a jami’ar, Bio ya ce ziyarar tasa a kasar Sin na da nufin karfafa huldar diflomasiyya da huldar tattalin arziki da cinikayya tsakanin kasahen biyu, tare da sa kaimi ga zurfafa mu’amala tsakanin jami’o’in kasashen biyu.
Ya kuma bayyana cewa tun lokacin da Saliyo ta shiga shirin shawarar “Ziri Daya da Hanya Daya” a shekarar 2018, kasar ta “ci gajiya sosai daga ayyukan da ke karkashin wannan shiri.
Hubei da Saliyo suna abokantaka na dogon lokaci. A cikin shekaru masu yawa, lardin ya aika da kwararrun masana aikin gona zuwa Saliyo don ba da gudmmawar kwarewa a fannin noma da dabarun kiwo. Haka kuma, jami’ar kimiyyar binciken kasa ta kasar Sin (Wuhan) ta ba da horo ga kwararru sama da 20 daga Saliyo a fannonin da suka hada da albarkatun kasa da aikin injiniya da kimiyyar muhalli da injiniyanci da sauransu. (Yahaya)