An daukin nauyin karatun matashin matukin Adaidaita Sahu nan na Jihar Kano, Awwalu Salisu da ya dawo da miliyan 15 da ya tsinta.
An dauki nauyin karatun matashin kan zunzurutun kudi har zuwa matakin digiri na biyu a kan kudi miliyan 250.
- HOTUNA: Yadda Taron Jaridar LEADERSHIP Na 2023 Ke Gudana A Abuja
- An Sulhunta Gwamnan Kano Da Sheikh Aminu Daurawa
Jaridar Leadership ta karrama Awwalu a ranar Talata a taronta na shekara-shekara a matsayin wanda ya lashe lambar yabo ta ‘Fitaccen Matashin LEADERSHIP’ na 2023 saboda nuna gaskiya.
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour (LP), Peter Obi ne, ya mika masa lambar yabo ta karramawa, tare da ba shi shaidar tallafin karatu a Jami’ar Baze da ke Abuja har zuwa matakin digiri na biyu.
Bayan haka, gwamnan Jihar Neja kuma wanda ya lashe lambar yabo ta GWAMNAN LEADERSHIP, Mohammed Umar Bago, ya jinjina wa jami’yyar LP kan rawar da ta taka a zaben 2023.
Bago ya sanar da bayar da tallafin karatu na Naira 250 ga Awwalu sakamakon nuna halin gaskiya da ya yi.
Ya ce Awwalu zai sake samun tallafin karatu na miliyan 50 daga wajensa, sannan ya ce shugaba Bola Tinubu, ministocin Nijeriya da sauran gwamnoni za su tallafawa matashin.
Bago ya kara da cewa zai sanya sunan daya daga cikin ayyukan titin da yake yi a Jihar Neja ga matukin Adaidaita sahun.