Mayakan Boko Haram sun kone sabbin gidajen da aka gina domin sake tsuganar da ’yan gudun hijira a Karamar Hukumar Dikwa a Jihar Borno.
Mayakan sun kutsa kauyen Gajibo da ke karamar hukumar ne suna harbi kan mai uwa da wabi sannan suka cinna wa sabbin gidaje 25 wuta.
- ‘Yansanda Sun Kama Shugaban Kungiyar Miyetti-Allah A Adamawa
- Gwamnan Kebbi Ya Raba Motoci 24 ga ‘Yan Majalisar Jihar
A ranar Lahadi kuma mayakan sun sace mutum 101; kananan ’yan mata 53 da samari 48 da suka je neman itacen girki a kauyen Gomboru Ngala.
Wani mazaunin yankin, Modu Kundiri, wanda ke hanyar zuwa Maiduguri daga Gomboru, ya ce sojoji sun dakatar da motocinsu na kusan awa uku a kauyen Logomani kafin daga bisani su bude hanya.
“Na ga akalla 25 daga cikin sabbin gidajen suna ci da wuta a kauyen Gajibo da ke yankin Dikwa,” in ji Modu.
Wani mazaunin garin Dikwa, Sheriff Lawan, wanda ya tabbatar da harin na safiyar ranar Talata da kuma kone gidajen, ya ce maharan sun dasa abubuwan fashewa a wurin da ake aikin ginin gidajen.
“Sojoji sun shaida mana cewa maharan sun dasa ababen fashewa a wajen, amma sojojin sun gano wasu bama-baman,” a garin na Gajibo mai nisan kilomita 110 daga Maiduguri, babban birnin jihar.