Gulimina Maimaiti, ’yar kabilar Uygur, ta kware wajen raye-rayen gargajiya na kananan kabilu daban daban. Ta yi fice ne a shekarar 2014 bayan ta lashe wata gasar shirin talabijin na raye-raye.
Ta zama ’yar rawa ta farko daga jihar Xinjiang ta Uygur mai cin gashin kanta dake arewa maso yammacin kasar Sin da ta yi rawa ita kadai a cibiyar wasannin fasaha ta kasar Sin dake Beijing. A matsayin mai jagorantar rawa irinta Xinjiang, rawar Gulimina mai burgewa, ya ja hankali sosai.
An haifi Gulimina Maimaiti a gundumar Dushanzi ta birnin Karamay dake Xinjiang a 1986. Ana kiran Xinjiang da “tekun raye raye da wake wake” bisa la’akari da galibin mazaunanta suna iya rawa da waka sosai. Gulimina ta fara bayyana basirarta ta rawa ne tun tana karama. A lokacin da take shekaru 6 da haihuwa ta fara koyon rawa a wata cibiyar fasaha ta yara, inda ta gane cewa rawa ba abu ne mai sauki ba. Ko mene ne dalili? Koyon dabarun rawa kamar mike kafa da raba su, ya ba ta wahala sosai. A wani lokaci, bitar na haifar mata da ciwon kafafu da har ya kai ta ga yin kuka, tana neman komawa gida.
Lallai akwai abun da ya ba ta kwarin gwiwa, a lokacin da take da shekaru 8 da haihuwa, ta kalli abokan karatunta suna rawa a talabijin yayin wata liyafa. Sai mahaifinta ya tambaye ta: “ko wata rana zan gan ki ki yi rawa a talabijin?” Gulimina ta ba shi amsa cewa, “na yi imanin zan yi rawa a talabijin wata rana. Ina so in zama babbar ’yar rawa, kuma a nan gaba, zan koyarwa yara yadda ake rawa.’’ Sannan, ta kara dagewa wajen koyon rawa, kuma hakan ya kai ta ga yin fice.
Malamar Gulimina ta farko mai suna Ayiguli, ta yi matukar kokari wajen horar da ita, kuma ta ba ta damammaki da dama na yin rawa. Gulimina ta ci kyauta ta farko a lokacin da take da shekaru 10 da haihuwa, yayin wata gasar rawa ta yara a Xinjiang. Da ta kai shekara 12, aka sanya ta a makarantar midil, dake karkashin Jami’ar wasannin fasaha ta Xinjiang, inda ta fara samun horon kwarewa a rawa. Horon ma ya fi wadanda ta yi a baya wahala. Gulimina ta dage sosai, don ko a lokacin hutu, ta kan shiga gasannin rawa.
A shekarar 2003, Gulimina ta shiga gasar Taoli, gasar rawa mafi koli a kasar Sin. Duk da cewa ba ta zo ta daya ba, ta gamsu abun da ta yi. Ta ce, “ban yi tsammanin samun damar shiga gasa kamar ta Taoli ba. Shiga matakin karshe na gasar ya ishe ni.”
Yayin da take kokarin ganin cimma burinta na zama fitacciyar ’yar rawa, ta shafe shekara 1 tana koyon wani salon rawa mai wahala na Uygur wato “Girl with a Bell” dake nufin yarinya mai kararrawa. A watan Mayun 2006, yayin da take shirin kammala gasar Taoli, ’ya’yarta ta fada mata cewa mahaifinsu na fama da matsalar shanyewar jiki kuma ya yi doguwar suma.
Nan da nan ta garzaya asibiti, inda ta zauna tana kula da shi tsawon wasu kwanaki. Ba ta ma son ta tuna da gasar. A wata rana, babanta ya farfado, sai Gulimina ta jiyo shi yana cewa, “Gulimina, na gan ki kina rawa a talabijin. Kin samu kyauta…..” daga nan ya sake shiga doguwar suma. A wannan lokaci, Gulimina ta fahimci abun da mahaifinta ke fata, don haka ta koma jami’a, ta ci gaba da bita tukuru. Ta kan yi bita na a kalla sa’o’i 10 a ko wace rana, wannan ya sa ta samu rauni a tafukan kafafunta. Amma duk da haka, ta shiga gasar ta Taoli, inda ta samu kyautar wadda ta zo ta biyu.
Tsakanin shekarar 2003 da 2009, Gulimina ta halarci gasanni da dama na kasa da kasa. Ta kuma samu kyaututtuka iri iri, baya ga haka, ta kara samun gogewa.
A shekarar 2009, Gulimina ta fara karbar dalibai masu koyon rawa. “A lokacin, na riga na samu sakamako masu kyau a gasannin rawa da dama. Bayan na zama karamar farfesa a sashen rawa na jami’ar wasannin fasaha ta Xinjiang, ina son mayar da hankali kan koyarwa maimakon shiga gasannin rawa”, a cewarta. Bisa kulawarta, dalibanta sun samu lambobin yabo da dama a shekarar 2012, yayin gasar kwararrun ’yan rawa ta kasa da aka yi a Hefei na lardin Anhui dake gabashin kasar Sin.
A shekarar 2014, an gayyaci Gulimina shiga wata gasar shirin talabijin da ake wa lakabi da “So You Think You Can Dance”. A fitowarta na farko a shirin, Gulimina ta burge alkalai da masu kallo da irin rawar kabilar Uygur. Ta bayyana kyan dake tattare da rawar ta hanyar basira da kwarewarta.
Wata fitacciyar ’yar rawar kasar Sin, kuma daya daga cikin alkalan wannan gasa, ta ce rawar Gulimina tamkar wani daftari ne na rawar Xinjiang. Ba tantama, Gulimina ce ta zo ta daya a gasar, inda kuma ta samu lakabin ’yar rawa mafi fice, a matakin karshe na gasar.
A watan Nuwamban 2021, Gulimina da tawagarta suka gabatar da wata dirama ta rawa mai suna Five Stars Rise from East, wato tashin taurari 5 daga gabas, a sanannen shirin talabijin na tashar CCTV3 mai suna National Treasure. Gulimina ita ce ta fito a matsayin jarumar diramar mai suna Chunjun, gimbiya daga yammacin yankin tsohuwar kasar Sin.
An kirkiro diramar ne daga wani kayan tarihi da aka gano a 1995, a lokacin da aka gano wani sulken hannu na daular Han (206BC–220AD) a wurin kiyaye tarihi na Niya dake Hotan na jihar Xinjiang. Diramar wadda ta bayyana taken hadin kan kasa, ta bayyana labarin wani janar na kabilar Han da wata gimbiya da suka kulla abota yayin da suka fuskanci kalubale tare.
Gulimina ta ce, “diramar na da muhimmanci a gare ni. Ya taimaka min wajen kara gane mahaifata, kuma ya sa ina jin cewa Xinjiang cibiya ce ta wake-wake da raye-raye da fasaha. Shi ne karo na farko da na yi diramar rawa. Na kara samun gogewa, kuma na koyi abubuwa daga sauran ’yan rawar da wadanda suka shirya diramar. Na kuma koyi tarihi da al’adu, wadanda ke da muhimmanci gare ni a matsayin malama.”
Gulimina ta zama karamar farfesa ce a kwalejin koyar da rawa ta jami’ar Minzu ta kasar Sin dake Beijing a shekarar 2020. Tana koyar da raye rayen gargajiya na kabilu daban daban da suka hada da Uygur da Kazakh da Uzbek da Tajik.
Gulimina ta ziyarci yankunan Sin da dama, domin gabatar da lakca a jami’o’i tare da shiga shirye shiryen al’umma da nufin yayata raye-rayen Xinjiang.
“Hakkina ne gadon rawar Xinjiang, da kuma koyar da yara masu sha’awar rawa dake tasowa. Xinjiang cibiya ce ta rawa da waka. Kabilu daban daban kan yi amfani da raye-raye da wake-wake wajen bayyana yanayin rayuwarsu da dabi’unsu da abubuwan dake zukatansu. A wajenmu, rawa da waka wata hanya ce ta fahimtar juna,” cewar Gulimina.
Bayan barkewar cutar COVID-19 a farkon 2020, Gulimina ta yanke shawarar gabatar da darusa ta intanet ga jama’a. Sama da mutane miliyan 1 ne suka halarci darasin da ta gabatar na yini 12, kana mutane sun kalli shirin sama da sau miliyan 20.
Yadda mutane suke sha’awar rawarta, ya taba zuciyar Gulimina, musamman yara daga yankuna maras ci gaba. Tana fatan kara gabatar da darusa ta intanet, domin karfafawa karin mutane gwiwar yin rawa, musamman yara.
“Na samu abubuwa da dama ta hanyar rawa, kuma ina godiya da hakan, domin rawa ne ya kai ni inda nake yanzu. Ina da tawagar ’yan rawa masu kwarewa, da iyali, kuma dukkansu na ba ni goyon baya. Na gamsu, domin su din dukiya ce gare ni… ina kuma fatan yayata wannan kuzari ta hanyar rawa da kuma taimakawa karin mabukata,” cewar Gulimina. (Kande Gao daga sashen Hausa na CMG)