Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Wang Wenbin, ya ce batun da ake kira da wai tarkon bashi na kasar Sin, batu ne kawai da masu adawa da dangantakar Sin da kasashe masu tasowa a Afrika da wasu yankuna don gaggauta samun ci gaba, suka kirkiro.
Wang Wenbin, ya bayyana haka ne yayin taron manema labarai na yau Laraba.
Rahotanni na cewa, wani rahoto da Gidauniyar Debt Justice ta Birtaniya, mai bibiyar harkokin da suka shafi bayar da bashi ba bisa adalci ba, ta fitar, ya zayyano wasu bayanai daga Bankin Duniya da asusun IMF da wasu cibiyoyi, inda suka nuna cewa, bashin da kasashen Afrika suka karba daga cibiyoyin kudi masu zaman kansu a kasashen yamma, sun ninka yawan bashin da suka karba daga kasar Sin hau sau 3, haka kuma kudin ruwansu ya ninka na Sin sau biyu. (Mai fassarawa: Fa’iza Mustapha daga CMG Hausa)