Gwamnatin Jihar Kaduna ta bayar da tabbacin cewa ba za ta lamunci wani malami ya yi amfani da mumbarinsa wajen cin zarafin wani ko addini da sunan tafsiri ba.
Bayanin hakan ya fito ne daga bakin mataimaki na musamman ga gwamnan Jihar Kaduna a bangaren harkar addini, Malam Abdulrahman Zakariyya, a zantawarsa da wakilinmu jim kadan bayan kammala taro da malamai masu wa’azi a Jihar Ka-duna wanda gwamnatin ta shirya musu.
- Kashi 70 Na Badakalar Kudade A Nijeriya Na Da Alaka Da Bankuna – EFCC
- Kano Za Ta Haɗa Gwiwa Da Afrinvest Don Haɓɓaka Kasuwanci Da Ci Gaban Jihar
Zakariyya, ya ce gamnatin Jihar Kaduna ta himmatu wajen ganin an samu zaman lafiya da hadin kan al’ummar jihar. Ya ce ba su amince da cin mutucin wani ko wasu ba a lokacin tafsirin watan Ramadana.
Ya ci gaba da cewa, “Gwamnatin Jihar Kaduna za ta tabbatar da cewa duk wanda zai yi wa’azi ya yi bayanai da za su taimaka wajen samar da zaman lafiya da hadin kan juna, sannan gwamnati ba za ta lamunci wani malami ya yi amfani da mumba-rinsa wajen cin zarafin wani ko addini da sunan tafsiri ba, saboda babu abin da gwamnati take fata wanda ya wuce samar da zaman lafiya da hadin kan al’umma baki daya.”