A yau 9 ga wata, Wu Qian, mai magana da yawun tawagar wakilan sojojin ‘yantar da jama’ar kasar Sin da rundunar ‘yan sandan kasar a zaman taro na biyu na majalisar wakilan jama’ar kasar Sin karo na 14, ya yi hira da manema labarai. Rahotanni sun bayyana cewa, manyan kasashe irin su Amurka, Japan, da Jamus sun kara yawan kudaden kashewa a fannin tsaro a wannan shekara ta 2024. Wasu manazarta na ganin cewa, sakamakon rikice-rikicen siyasa na kasa da kasa, duniya na cikin wani yanayin na bunkasar kudaden aikin soja.
Game da wannan, Wu Qian ya gabatar da cewa, kasafin kudin tsaron kasar Sin na bana ya karu da kashi 7.2 cikin dari idan aka kwatanta da adadin da aka kashe a bara, wanda yake a bayyane, da gaskiya, mai ma’ana, kuma matsakaici. (Yahaya)