Hajiya (Dr) Maryam Abacha, uwargidan tsohon shugaban kasar Nijeriya, Marigayi Sani Abacha, ta yi kira ga gwamnoni da sauran al’umma masu hannu da shuni da su siya kayayyakin abinci su tallafa wa al’umma marasa karfi, musamman a daidai wannan lokaci da ake fuskantar watan Ramadan.
Hajiya Maryam ta bayyana hakan ne lokacin da take tattaunawa da ‘yan jarida a gidanta da ke Kano a yayin addu’ar tunawa da shekara daya da rasuwar danta Abdullahi.
- Fasa-kwaurin Abinci: Gwamnati Ta Cafke Motocin Dakon Hatsi 141
- An Kammala Canja Fasalin Gasar Cin Kofin Zakarun Turai
Hajiya Maryam ta lurantar da cewa al’umma a halin yanzu suna cikin wani yanayi da suke da matukar bukatar taimako, inda ta ja hankalin gwamnoni da su yi amfani da karin kudaden da gwamnatin tarayya ta ba su wajen hidimta wa al’umma.
“Ina kira ga gwamnatoci da al’umma da su taimaka wa jama’a. A gaskiya akwai rashin kudi. Akwai abinci amma ya yi tsada ga karancin kudi.
“Don Allah jama’a a taimaka. Masu kudi da gwamnati su taimaka. Kuma na ji dadi sosai da aka ce shugaban kasa ya ba gwamnoni kudi da yawa. Allah ya sa su yi amfani da shi yadda ya dace. A siya hatsi a raba wa marasa karfi a cikin al’umma.
“Masu karfi kowa ya yi kokari ya harhada ya tallafa. Haka addinin Musulunci ya ce, haka addinin kirista ya ce. Ka ga kowa zai samu idan aka yi hakan. Allah ya sa a yi.
“Allah ya sa mu riski watan Ramadan da rai da lafiya. Watan Ramadan da mai rai da lafiya kullum shekara ana yi. Allah ya sa mu samu wannan lafiya, da ranmu da lafiyarmu ya sa a yi damu”, in ji ta