Madabba’ar harsunan waje ta kasar Sin ta wallafa littafi na 1 da na 2 na littafin “Zababbun Kalamai Daga Jawaban Xi Jinping” cikin harshen Ingilishi, wato “Selected Readings from the Works of Xi Jinping”, domin rabawa a cikin gida da ma kasashen waje.
Littattafan 2 na kunshe da muhimman jawaban shugaba Xi Jinping daga watan Nuwamban shekarar 2012 zuwa Oktoban shekarar 2022.
Wallafa littattafan 2 cikin harshen Ingilishi, na da matukar muhimmanci ga al’ummun duniya wajen fahimtar tsarin zamanantar da kasar Sin da ma wayewar kan kasar a wannan zamani. (Fa’iza)