Hukumar kula da wutar lantarki ta Kaduna (KE) ta mayar da martani kan yajin aikin da ‘yan kungiyar ma’aikatan wutar lantarki ta Nijeriya (NUEE) suka shiga, inda ta bayyana shirin a matsayin wanda sam bai dace ba, kuma ya kamata duk ‘yan Nijeriya masu kishin kasa su yi Allah-wadai da shi.
Kamfanin samar da Wutar Lantarki na kasa (DisCo) ya bayyana cewa, yajin aikin da ma’aikatan wutar lantarkin suka fara a farkon watan Ramadan zai haifar da rashin jin dadi ga ‘yan Nijeriya musamman a irin wannan lokaci.
- Wainar Da Aka Toya A Taron Majalisar Zartarwar Jihar Zamfara Na 18
- Ma’aikatan Kamfanin Samar Da Lantarkin Kaduna Sun Tsunduma Yajin Aikin Sai Baba Ta Gani
In ba a manta ba, mun rahoto muku cewa, Kungiyar ma’aikatan wutar lantarki ta kasa (NUEE), reshen jihar Kaduna, ta tsunduma yajin aikin sai baba-ta-gani a ranar Talata kan kin tura wa mambobinta kudaden fansho, watsar da batun karin girma da sauransu.
Kungiyar a cikin sanarwar da ta aike wa shugabannin kungiyar kwadago ta Nijeriya (NLC) a Kaduna dauke da sa hannun sakataren kungiyar, Kwamared Ado Ali, ta zargi mahukuntan kamfanin rarraba wutar lantarki na Kaduna da rashin tura kudaden fansho ga ma’aikata sama da 3000 a asusun ajiyarsu na fansho har tsawon watanni fiye da 72.