Ma’aikatan kamfanin samar da wutar lantarki na Jihar Kaduna, sun yi zanga-zanga a hedikwatar kamfanin tare da shiga yajin aikin sai yadda hali ya yi.
Ma’aikatan da ke karkashin kungiyar ma’aikatan kamfanonin wwutar lantarki (NUEE), sun toshe hanyar shiga ofishin wanda ya haifar da hana shigar mutane.
- Gobara Ta Hallaka Yara 2 A Sansanin ‘Yan Gudun Hijira A Borno
- Tinubu Ya Umarci Jihohi Su Bai Wa Ma’aikata Kyautar Kudin Rage Radadi
Ɗaya daga cikin masu zanga-zangar, ya ce a yanzu an kwashe kimanin shekaru shida ba a saka musu kuɗinsu na fansho a asusun ajiyarsu ba, tare kuma da rashin biyan haƙƙoƙin waɗanda suka rasu a lokacin da suke wa kamfanin aiki, kazalika da kuma dakatar da wasu ma’aikata bakwai da kuma shirin dakatar da mutane 1000 daga aikinsu.
A lokacin da sakataren kungiyar, Ayuba Pukat yake jawabi ya bayyana abin da kamfanin ke yi wa ma’aikatan a matsayin rashin adalci.
Ya ce “Mun zo nan ne domin neman ‘yancinmu daga kamfanin samar da wutar lantarki na Kaduna, duba da irin abubuwan da ke faruwa marasa dadi gare mu ma’aikata”.
Ya ƙara da cewa “Yanzu fa kimanin watanni 72 ba a saka mana kuɗin fanshonmu ba a asusun ajiyarmu, wanda wannan ba ƙaramin laifi ba ne, don haka muna kira da a kwace lasisin kamfanin.
“Hakazalika sun dakatar da ma’aikata 14 ta dalilin lalacewa kayan aiki da suka samu a ƙaramar Hukumar Zariya.”
Sai dai mai magana da yawun kamfanin, Abdulazeez Abdullahi, ya ce sun yi Allah-wadai da matakin da ma’aikatan suka dauka na yin zanga-zanga tare kuma da rufe hanyoyin shiga ofishin.
Ya ce a yanzu haka sun riga da sun saka ranar Laraba a matsayin ranar da za su zauna da ƙungiyar domin tattaunawa da su kan haƙƙokinsu na fansho da kuma yadda za a shawo kan matsalar.