A ranar Litinin ne gwamnatin jihar Anambra ta rusa akalla shaguna 2,000 da ke kan titin Neja a garin Fegge a karamar hukumar Onitsha ta Kudu a jihar.
Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya, NAN ya ruwaito cewa, ruguza shagunan ya zama dole biyo bayan rugujewar wani bene mai hawa biyar da ake ginawa a titin Basden a garin Fegge.
- Ma’aikatan Kamfanin Samar Da Lantarkin Kaduna Sun Tsunduma Yajin Aikin Sai Baba Ta Gani
- Kasar Sin Na Taimakawa Kasashen Afirka Bunkasa Sabon Karfin Samar Da Hajoji Da Hidimomi Masu Karko
Shugaban karamar hukumar Onitsha ta Kudu, Mista Emeka Orji, wanda ya jagoranci ruguja shagunan, ya shaida wa manema labarai cewa, ya bi umarnin Gwamna Charles Soludo ne wurin ruguza shagunan.
Ya ce, an bayar da sanarwa game da rusau din amma masu shagunan suka bijire wa sanarwar.