Barcelona ta kai wasan daf da na kusa da na karshe a gasar cin kofin zakarun Turai a karon farko cikin shekaru hudu, bayan da ta yi nasara a kan Napoli a ranar Talata.
Fermin Lopez da Joao Cancelo ne suka ci wa Barcelona kwallo a filin wasa na Estadi de Montjuic, sai dai masu masaukin baki sun yi kokari matuka bayan da Napoli ta zura kwallo ta hannun Amir Rrahmani.
- Da Ɗumi-ɗuminsa: ‘Yan Bindigar Da Suka Sace Ɗaliban Kuriga Na Neman Fansar Naira Tiriliyan 1
- Sin Ba Ta Amince Amurka Ta Samarwa Yankin Taiwan Makamai Ba
Bayan dawowa daga hutun rabin lokaci dan wasan gaba na kasar Poland, Robert Lewandowski ya jefa kwallo a ragar Napoli ana saura minti bakwai a tashi daga wasa.
A ranar Juma’a ne za a rava jadawalin gasar zakarun Turai, inda kowa zai san wanda zai hadu da shi a zagayen dab da na kusa da na karshe.