Majalisar dattawan Nijeriya ta dakatar da shugaban kungiyar sanatocin arewa, Abdul Ningi na tsawon watanni uku bisa zargin an cusa Naira tiriliyan 3.7 a cikin kasafin kudin 2024.
Shugaban majalisar dattawan, Sanata Godswill Akpabio ne ya sanar da daukan wannan mataki a zaman majalisar da ya gudana bayan sauraron korafin da aka shigar a kansa.
- Ci Gaban Kasar Sin Na Ingiza Bunkasar Tattalin Arzikin Duniya
- Ba Za A Iya Dakatar Da Dunkulewar Kasar Sin Ba
Mamba a kwamitin kasain kudi na majaliar dattawa, Sanata Jimoh Ibrahim, mai wakiltar Ondo ta kutu, shi ne ya fara gabatar da kudurin dakatar da Sanata Ningi na tsawon wata 12, bisa zarginsa da ba da bayanai karya wanda suke daidai da aikata babban laifi, da kuma hargitsa zaman lafiya a zauren majalisar dokokin kasa.
Sanata Ede Daminone, mai wakiltar Delta ta tsakiya, ya bayyana cewa tun dai an bai wa Sanata Ningi damar bayar da hakuri kuma ya ki, to shi ya goyi bayan kurin dakatar da shi na tsawon watanni 12.
Amma Sanata Asukuo Ekpenyong, mai wakiltar Kuros Riba ta kudu ya bukaci a dakatar da Sanata Ningi na tsawon wata 6, yayin da Sanata Buhari Abdulfatai ya amince a dakatar da shi na tsawon wata 3.
Sanata Garba Musa Maidoki, mai wakiltar Kebbi ta kudu ya amince da dakatar da Ningi har tsawon wata 3 tun da dai ya bayyana kalaman da ba daidai ba kuma ya ki bayar da hakuri.
A nasa bangaren, Sanata Sani Musa, mai wakiltar Neja ta gabas, ya ce a takatar da Sanata Ningi na tsawon watanni uku tare da ba shi damar rubuta wasikar bayar da hakuri.
Bayan jin ra’ayoyin ‘yan majalisar, daga karshe dai shugaban majalisar dattawan, Sanata Godswill Akpabio ya takatar da Sanata Ningi daga majalisa na tsawon wata 3.
Nan take Sanata Ningi ya bar zauren majalisar dattawan tare da daukar takardunsa a hannu, yayin da wani dogarin majalisan yana yi masa rakiya har zuwa waje.
Wannan lamari ya janyo cece-ku-ce a zauren majalisa a ranar Talata da ta gabata, wanda ake ganin cewa Sanata Ningi ya fare laya, yayin da ita kuma majalisa ta sagale shi na wata 3.
Shugaban majalisan ya yanke wannan hukunci ne bisa dogaro da sashi na 66 (1) da kuma sahi na 2, wadanda suka bai wa shugaban majalisa karfin ikon ladaftar da duk wani ‘yan majalisa da ya yi laifi tare da bai wa dokarin majalisa damar fitar da shi waje.
Kazalika, Sanata Ningi ya sauka daga mukaminsa na shugaban kungiyar sanatocin arewa.
A cikin wata sanarwa da ya fitar, Sanata Ningi, wanda shi ne shugaban kwamitin kidaya na majalisar dattaea, ya bayyana murabus dinsa daga shugabancin kungiyar sanatocin arewa.
A cikin wasikar da aka bai wa sakataren kungiyar sanatocin arewa mai taken yin murabus, Sanata Ningi ya ce yin murabus dinsa ya sama wajibi bisa abubuwa da suke faruwa a halin yanzu.
“Ina mai mika godiyata ta musamman ga kungiyar sanatocin arewa da suka ba ni dama na shugabanci na tsawon wata 8, a wannan muhimmin kungiya. Ina da yakinin cewa wannan kungiya tana da matukar muhimmanci wajen kawo abubuwan da za su bunkasa yankin arewacin Nijeriya,” in ji Ningi.
Jerin Sanatocin Da Aka Dakatar Tun Daga 1999
An dakatar da sanatan Ogun ta tsakiya, Femi Okurounmu a 1999.
Laifinsa: An zarge shi da tunzura sanatoci wajen shirin tsige Obasanjo.
Haka kuma an dakatar da sanata mai wakiltar Benuwai ta arewa, Joseph Waku, a watan Fabrairun 2000.
Laifin da ya aikata: Yana kira da a yi juyin mulki bayan komawa mulkin dimokuradiyya da wata 8.
An dakatar da sanatan Imo ta yamma, Arthur Nzeribe a watan Oktoban 2002.
Laifinsa: Yin wasu ayyuka da ba su dace ba a majalisa.
Sannan an dakatar da sanatan Neja ta tsakiya, Isah Mohammed a watan Oktoban 2004.
Laifinsa: Marin Sanata Iyabo Anisulowo.
An dakatar da sanatan Borno ta kudu, Ali Ndume a 2017.
Laifinsa: Shigo da motocin kirar Range Robe da takardun bogi bisa sa sunan Bukola Saraki kuma na Dino Melaye ne.
An dakatar da sanatan Delta ta tsakiya, Obie Omo-Agege a 2018, bisa jagorantar wata tawaga da take a dawa da shugaban majalisar dattawa.
Haka kuma an dakatar da sanatan Bauch ta tsakiya, Abdul Ningi. An dakatar da shi ne a 2024 bisa bayar da bayanan karya kan aringizon kasafin kudin 2024 na naira tiriliyan 3.7.