Yayin da Ghana ke shirin karbar bakuncin gasar wasannin Afirka da aka jinkirta a shekarar 2023, masu shirya wasannin cikin gida sun kwara ruwan sanyi kan fargabar da ake yi, inda suka ce kasar ta shirya tsaf domin gudanar da gasar wasannin.
An dage wasannin da aka shirya gudanarwa a watan Agustan shekarar 2023 saboda rashin daidaito da aka samu kan hakkin tallace-tallace wanda ya kawo tsaikon kammala filayen gudanar da wasannin, tare da rashin jituwa tsakanin kungiyoyin da suka hada da masu shirya gasar, da ta tarayyar Afrika (AU), da kungiyar kwamitocin Olympics na Afirka (Anoca) da kuma kungiyar hukumomin wasannin Afrika.
- Kafa Jam’iyyar Adawa: Atiku Da Wasu Sanatoci Sun Sake Sabon Yunkuri
- Kabilu Biyar Mafiya Tsadar Aure A Nijeriya
Duka kungiyoyi uku na taka muhimmiyar rawa wajen shirya gasar wanda a yanzu aka shirya aka fara gasar a Accra a ranar 8 ga Maris, a kuma kammala ranar 23 ga watan na Maris.
Mai magana da yawun kwamitin shirya wasannin na Afirka (LOC), Dan Kwaku Yeboah, ya bayyana cewa wannan wata dama ce ta musamman a gare su, su kasar Ghana domin yin abin a zo a gani.
Ya ce “An fara gudanar da wasannin Afirka ne tun a shekarar 1965, kuma in ban da Nijeriya babu wata kasa ta yammacin Afirka da ta samu damar karbar bakuncin gasar gaba daya.
Yeboah ya kara da cewa suna shirye daga kowane bangare, daga ababen more rayuwa da masauki da sufuri da kafofin yada labarai kuma kowanne tsari yana kan hanya sai dai an dan jinkirta aikin tantancewa.
Daya daga cikin tawagogin da tafiyar hawainiyar tantancewar ta shafa ita ce kasar Kamaru, wanda ‘yan wasa da jami’anta da na kafofin yada labarai suka fuskanci karancin lokaci wurin tabbatar da matsayinsu a Ghana.
Amma Sakataren Kwamitin Wasannin Olympic na Kamaru, Dabid Ojong ya ce da farko jami’insu ya samu ‘yan matsaloli wajen fahimtar yadda ake aiki da dandalin tantancewar, amma yayin wani zama da ya yi da LOC ta Intanet, an ba shi haske kan yadda dandalin ke aiki.
Yayin da aka fara gasar a hukumance, an kuma nuna damuwa kan yadda Ghana za ta iya gudanar da wasannin duba da irin halin tattalin arzikin da kasar take ciki.
Wani mai sharhi kan harkokin wasanni na Afirka ta Kudu, Duane Dell’Oca ya ce, har wani bangaren filin motsa jiki ya fara lalacewa inda ya fara nuna alamun tsagewa, kuma makonni kadan da suka gabata aka shimfida shi.
Matsalar rashin manyan taurarin afirka a gasar
An tabbatar da wasanni 29 a gasar wasannin ta Afrika, da wasannin guje-guje da tsalle-tsalle, da wasan kwallon badminton, da tseren keke, da ninkaya, da wasan tennis, da kuma kokawa, domin zama na masu neman cancantar shiga gasar Olympics a Birnin Paris 2024.
Duk da haka, lokacin gudanar da wasannin na nufin da yawa daga cikin fitattun masu fafatawa a Afirka ba za su halarta ba, wannan babbar matsala ce ga wadanda ke tallata gasar, a cewar Dell’Oca. Dell’Oca ya ce ba su samu damar tallata hotunan manyan ‘yan wasan Afirka da yawa ba saboda an samu rudani sosai kan wadanda za su fafata a gasar kuma hakan babbar barazana ce.
Tsohuwar ‘yar wasan Bolley Ball ta Kenya Jannet Wanja, wadda a yanzu ita ce mai horar da ‘yan wasan kasar, ita ma ta koka kan rashin samun halarcin manyan taurarin ‘yan wasa.
Ta ce a lokuta da yawa wasannin sun samu koma baya saboda rashin manyan ‘yan wasa da taurari da za su iya karawa gasar daraja, kuma sau da yawa ana hana manyan ‘yan wasa zuwa wanda kuma hakan ba ya taimakawa kuma Afirka ma tana da mahimmanci.
Ta ci gaba da cewa duk da kalubalen da ake fuskanta a gasar, tana da kwarin gwiwar samun nasarar gudanar da gasar wasannin Afirka a Ghana kuma yawancin kasashe har yanzu suna fama da tasirin cutar Korona, sannan matakan shirye-shiryensu sun yi kasa da abin da ake bukata, amma har yanzu tana fatan samun nasarar gasar.
Ojong ya ce, duk fargabar da ake yi game da filayen wasa da kayan aiki, dukkanin kungiyoyi za su fuskanci batutuwa iri daya.
“Idan LOC da kungiyoyin kasa da kasa sun tabbatar da cewa filayen sun dace da wasa, dole ne tawagogi su yi wasa a filayen yadda su ke.” in ji shi.
“Kowa zai yi wasa a wuri guda, kowa zai fukanci matsaloli iri daya, kuma hakan zai zama wani bangare na wasan.”
Ghana tana matukar farin ciki
Bayan murnar gasar cin kofin nahiyar Afirka da aka kammala kwanan nan a kasar Ibory Coast, Yeboah ya ce ya kamata ‘yan kallo da ‘yan wasa da jami’ai su sa rai cewa za a gudanar da gasar da ba za a manta da ita ba a nahiyar Afirka.
Ya kara da cewa ya kamata Afirka ta yi tsammaci irin karamci da al’adun Ghana da aka saba gani – su yi tsammanin za a gudanar da bikin bude gasa mai matukar kayatarwa kuma ya kamata su kyautata zaton ganin wasanni masu kayatarwa da kuma kyakkyawan yanayi a tattare da gasar saboda ‘yan Ghana na cikin matukar farin ciki.
Ana sa ran manyan wakilan kungiyar AU da shugabannin kasashe daban-daban da kuma ‘yan wasa sama da 5,000 da jami’ai daga sassan nahiyar su halarci gasar wanda za a shafe tsawon mako biyu ana gudanarwa.