Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya aza harsashin gina asibitin ido da hakora a garin Biu, da ke karamar hukumar Biu ta jihar.
Asibitin idon, zai kunshi dakunan tiyata guda biyu, dakunan tuntuba, bangaren gudanarwa, da kuma dakunan maza da mata wadanda ke da gadaje 56 sannan kuma, asibitin hakori, za a samar da dukkan kayan aikin da ake bukata don ba da kulawa ga lafiyar hakori.
- Zulum Ya Ƙaddamar Da Sabuwar Kasuwar Banki Da Rikicin Boko Haram Ya Ɗaiɗaita
- Zulum Ya Daukaka Darajar Kwalejin Larabci Zuwa Babbar Cibiyar Yaki Da Akidun Boko Haram
Zulum, yayin da yake gargadin ‘yan kwangilar da su tabbatar da bin ka’idojin aiki, ya gindaya watanni shida don kammala aikin.
Gwamnan ya bayyana cewa, gwamnatinsa ta amince da gina wasu asibitocin ido da na hakori guda biyu da za a yi a kudanci da arewacin Borno domin su karfafa na birnin Maiduguri.